Da duminsa: An bindige Damina, dan bindigan da ya kona mata da ran ta a Zamfara

Da duminsa: An bindige Damina, dan bindigan da ya kona mata da ran ta a Zamfara

  • Kungiyar 'yan bindiga ta Dogo Gide ta bindige gagararren dan bindigan da ya addabi Dansadau da kewaye mai suna Damina
  • Damina fitaccen dan bindiga ne da ya taba kona wata mata da ran ta a Dansadau kuma ya shahara a saka wa jama'a haraji
  • An gano cewa, Dogo Gide ya aike masa da jan kunne kan ya daina kisan da ya ke, amma ya ki, hakan ta sa ya tare shi tare da halaka shi

Zamfara - Damina, wani gagararren dan bindiga kuma shugaban barayin shanu a jihar Zamfara, an bindige shi har lahira.

Mamacin wanda ke da sansani a dajin Kuyanbana da ke masarautar Dansadau a karamar hukumar Maru ta jihar Zamfara, ya taba kona wata mata da ran ta yayin daya daga cikin farmakin da ya kai.

Kara karanta wannan

Sabon hari: 'Yan bindiga sun kai hari masallaci, sun bindige masallata a jihar Neja

Da duminsa: An bindige Damina, dan bindigan da ya kona mata da ran ta a Zamfara
Da duminsa: An bindige Damina, dan bindigan da ya kona mata da ran ta a Zamfara
Asali: Original

An kashe Damina ne sakamakon wata arangama da yayi da kungiyar 'yan bindigan da Dogo Gide ke shugabanta.

Daily Trust ta tattaro cewa, mamacin dan bindigan ne ke da alhakin wasu miyagun farmaki, satar mutane, satar shanu da kuma kallafa wa jama'ar yankunan haraji a Dansadau da ke jihar.

A watan Yulin da ta gabata, Damina ya kai farmaki kauyukan Tungar Baushe da Randa, inda aka kashe mutane masu tarin yawa da mazauna yankin kusan dari.

Har ila yau, a wannan farmakin, sun sace mata masu yawa tare da kananan yara.

Majiyoyi sun sanar da Daily Trust cewa, Damina ya mutu ne sakamakon miyagun raunikan da ya samu sakamakon arangamar da suka yi da kungiyar Dogo Gide kusa da Chilin da Fammaje, yankunan noma da ke karkashin ikonsa.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Basirar fasihin makaho ta burge Ganduje, ya bashi aiki nan take

Wata majiya ta ce Dogo Gide, wanda ke da alaka da 'yan ta'addan ISWAP, sun kai farmaki bayan an kai musu korafi kan yadda Damina ke kisan jama'a tare da hana su sakat.

Kamar yadda majiyoyi da suka san aukuwar lamarin suka ce, Dogo Gide ya aike da jan kunne ga Damina kan ya daina kai farmaki yankunan kuma ya daina kashe manoma, amma ya ki jin jan kunnen.

Fusatattun Zamfarawa sun mamaye titunan jihar, suna zanga-zangar rashin tsaro

A wani labari na daban, fusatattun mazauna kauyukan karamar hukumar Tsafe ta jihar Zamfara a ranar Laraba sun rufe babban titin Gusau zuwa Funtua domin bayyana fusatarsu kan al'amuran 'yan bindiga a jihar.

Mazauna yankin sun ce ba za su bar ababen hawa da jama'a wucewa ba har sai an yi maganin kokensu, Daily Trust ta wallafa.

Sun ce duk da datse layukan sadarwa da aka yi a jihar, miyagun 'yan ta'adda sun hana su zuwa gonakinsu, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Tsoro da zaman dardar: Yadda shirin NYSC ya zama abin tsaro ga 'yan bautar kasa

Asali: Legit.ng

Online view pixel