Yanzu-yanzu: Bayan zaman jiran tsammani, An saki sakamakon jarabawar NECO

Yanzu-yanzu: Bayan zaman jiran tsammani, An saki sakamakon jarabawar NECO

  • Bayan watanni dalibai na zaman jiran tsammani, hukumar NECO ta saki sakamakon jarabawar da suka zana
  • Shugaban hukumar ya bayyana cewa mutum dubu bakwai kadai ne basu zana jarabawar ba duk da sun yi rajista
  • An dakatad da wasu makarantu da Malamai da aka kama dumu-dumu suna rashawa da magudin zabe

Minna - Hukumar shirya jarabawar fita daga sakandare ta Najeriya watau NECO ta saki sakamakon jarabawar kammala karatun sakandare na shekarar 2021.

Shugaban hukumar, Farfesa Dantani Ibrahim Wushishi, ya sanar da hakan a hedkwatar hukumar dake Minna, jihar Neja ranar Juma'a, rahoton DailyTrust.

A jawabin da ya saki, ya bayyana cewa cikin dalibai 1,233,631 da suka yi rijistan yin jarabawar na bana, mutum 1,226,796 suka samu nasarar rubutawa.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Osinbajo da Tinubu sun hadu ana tsaka da rade-radin baraka a tsakaninsu

A cewarsa, adadin daliban ya hada da Maza 657,389 da kuma Mata 576,242.

Farfesa Wushishi ya kara da cewa cikin wadannan dalibai, mutum 878, 925 suka samu nasarar samun akalla makin 'C' a maddodi 5 wanda ya hada da Turanci da Lissafi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An saki sakamakon jarabawar NECO
Yanzu-yanzu: Bayan zaman jiran tsammani, An saki sakamakon jarabawar NECO Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Hakazalika ya bayyana cewa an damke mutum 20,003 kan laifin magudi da satar amsa lokacin jarabawar, riwayar Thecable.

A jihar Bauchi, Kaduna da Bayelsa, an dakatar da makaranta daya na tsawon shekaru biyu bisa laifin taimakawa dalibai wajen satar amsa, a cewarsa.

A jihar Katsina kuwa, makarantu biyu aka dakatar, ya kara.

Bugu da kari, an dakatad da Malamai 20 kan laifin taimakawa wajen yin magudi.

Yace:

"An dakatad da Malamai masu lura da dalibai 20 kan laifin ha'inci wajen aikinsu, taimakawa wajen magudin jarabawa, hada kai da wanda ba dalibai ba da rubuta musu amsa kan allo da kuma amsan rashawa."

Kara karanta wannan

Allah Ya yiwa marubucin littafin 'Kulba na barna', Umaru Kasagi, rasuwa

Jerin mutane 6 da ke da hannu a yawaitar magudin jarrabawa, Prof. Salisu Shehu

Farfesa Salisu Shehu, shugaban jami'ar Al-Istiqama da ke Sumaila a jihar Kano ya bayyana tushen matsalar magudin jarrabawa a kamarantun Arewacin Najeriya.

Farfesa ya bayyana hake yayin wata hira da wakilinmu na Legit.ng Hausa a farkon makon nan, inda ya bude maganganu da yawa da suke da alaka da karantarwa da ma harkar tabarbarewar ilimi a yankin Arewa.

A bayanansa, ya danganta laifin satar jarrabawa ga wadannan bangarori guda shida kamar haka: Gwamnati, Hukumomin ilimi, shugabannin makarantu, Malamai, iyaye, da dalibai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel