Borno: Dakarun soji sun halaka 'yan ta'adda masu hada bam daga takin zamani

Borno: Dakarun soji sun halaka 'yan ta'adda masu hada bam daga takin zamani

  • Sojojin rundunar Operation HADIN KAI sun sheke wasu 'yan ta'adda da ke hada bama-bamai da takin zamani
  • An halaka 'yan ta'adda a kauyukan Dar, Kumshe, Wulgo, Chabbol da Kijmatari duk a jihar Borno
  • Duk a cikin lokacin, 'yan ta'adda 1,199 ne suka mika makamansu yayin da aka kashe wasu miyagun 38

Borno - Dakarun sojin Najeriya da ke aiki da rundunar Operation HADIN KAI sun halaka wasu 'yan ta'adda tare da samo a kalla motocin yaki biyu tare da buhunan taki 622 da suke amfani da shi wurin hada bama-bamai.

An halaka 'yan ta'addan a sassa daban-daban na jihar Borno da suka hada da kauyukan: Dar, Kumshe, Wulgo, Chabbol da Kijmatari duk a jihar Borno da kuma titunan Ngala zuwa Wulgo da Nguru zuwa Kano.

Kara karanta wannan

An cire jami'an hukumar shiga da fice da Kwantrola Janar ya kama suna rashawa lokacin da yayi basaja

Borno: Dakarun soji sun halaka 'yan ta'adda masu hada bam daga takin zamani
Borno: Dakarun soji sun halaka 'yan ta'adda masu hada bam daga takin zamani. Hoto dailynigerian.com
Asali: UGC

Mukaddashin yada labaran tsaro, Birgediya Janar Benard Onyeuko, ya bayyana hakan ga manema labarai a Abuja a ranar Lahadi, Daily Trust ta wallafa.

"A yayin ayyuka cikin wannan lokacin, an halaka 'yan ta'adda 38 da suka hada da sabon shugaban ISWAP, Bako," yace.

Hakazalika, 'yan ta'adda 11, masu kai musu bayanan sirri da kuma masu samar musu da kayayyakin bukata duk an kama su yayin aikin.

A cewarsa:

"An samu karin miyagun makamai 29, carbin harsasai 166 da wasu miyagun makamai. Sauran sun hada da motocin yaki 2 da buhunan taki 622 da suke amfani da shi wurin samar da bama-bamai. An ceto wasu farar hula 5 da aka yi garkuwa da su."

Daily Trust ta ruwaito cewa, ya kara da cewa, tsakanin 15 zuwa 28 ga watan Oktoban 2021, 'yan ta'adda 1,199 tare da iyalansu suka mika wuya ga sojoji.

Kara karanta wannan

Dattawan Arewa sun tafi kotu, sun bukaci a raba Najeriya, a ware 'yan wani yankin kudu

Akwai magidantan maza 114, mata manya 312 da yara kanana 713 daga sassa daban-daban na yankin arewa maso gabas.

Jiragen NAF sun yi wa 'yan ISWAP luguden wuta yayin da suke cikin jiragen ruwa 11

A wani labari na daban, Jiragen yakin dakarun sojin sama na Najeriya, NAF, sun ragargaji wasu mayakan ta'addanci na ISWAP a yankin arewa maso gabas. PRNigeria ta tattaro cewa jiragen saman sun saki ruwan wutar ne a tsibirin Tumbun, kusa da tafkin Chadi.

Wata majiyar rundunar sojin, ta ce bayan bayanai kwarara na sirri kan cewa mayakan ISWAP suna tattaruwa domin wani gagarumin taro a tsibirin Tumbun.

Hakan yasa jiragen yaki karkashin Operation Hadin Kai suka shirya tsaf tare da sakar musu ruwan wuta, Daily Nigerian ta wallafa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel