An cire jami'an hukumar shiga da fice da Kwantrola Janar ya kama suna rashawa lokacin da yayi basaja

An cire jami'an hukumar shiga da fice da Kwantrola Janar ya kama suna rashawa lokacin da yayi basaja

  • An hukunta jami'an hukumar da aka kama dumu-dumu suna cin hanci da rashawa a jihar Legas
  • Mukaddashin Shugaban hukumar ne ya kamasu lokacin da yayi shigan burtu ya kai ziyarar bazata
  • Akalla mutum hudu suka rasa kujerunsu a sabon garambawul da akayi a hukumar

Legas - Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa an cire jami'in bada fasfot a ofishin hukumar shiga da fice dake Ikoyi jihar Legas, DCI Ibrahim Liman.

Wannan ya biyo bayan ziyarar da mukaddashin kwantrola janar na hukumar, Isa Jere, ya kai ofishin yayi inda basaja basu ganesa ba ya kamasu dumu-dumu suna rashawa.

Bayan Liman, an cire abokan aikinsa dake ofishin Ikeja, N.J Dashe, da kuma Adeola Adesokan na FESTAC.

Tuni na mayar da Ibrahim Liman da Adeola Adesokan hedkwata Abuja, yayinda shi kuma N.J Dashe aka mayar da shi 'A' Command.

Kara karanta wannan

Jami'an tsaro sun ceci mutumin da ya hau hatsumiya yana kokarin kashe kansa a Legas

Sauran jami'an da abin ya shafa sune A.I Bambale, wanda aka mayar tashar jirgin Nnamdi Azikwe dake Abuja daga zone 'A'.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An cire jami'an hukumar shiga da fice da Kwantrola Janar ya kama suna rashawa lokacin da yayi basaja
An cire jami'an hukumar shiga da fice da Kwantrola Janar ya kama suna rashawa lokacin da yayi basaja Hoto: NIS
Asali: UGC

Wadanda suka maye gurbinsu

Ba tare da bata lokaci ba, an maye gurbin Liman da Abolupe Oladoyin Bewaji yayinda aka maye gurbin Mr Dashe da Mrs Adesokan da R.L Bukar da S. Umar.

Mataimakin kwantrola janar. A.B Yarima, ya bayyana hakan a takardar da ya saki.

An maye Bambale kuwa da Sunday James, wanda shine tsohon Kakakin hukumar.

Yadda shugaba a NIS ya yi shigan burtu ya kame jami'ansa dumu-dumu da rashawa

Mukaddashin Kwanturola Janar na Hukumar, Isa Jere Idris, ya cafke wasu jami’an hukumarsa dumu-dumu a kokarinsu na hada harkallar badakala.

Idris wanda ya yi shigar burtu a matsayin mai neman fasfo na kasa da kasa a a ofishin rundunar da kejihar Legas, ya kama su lokacin da suka yi masa tayin taimaka masa wajen siyan fasfo din ta hanyar da bata dace ba.

Kara karanta wannan

Shugaban Marasa Ji Marlians na cigaba da gurfana a kotu kan zargin damfarar yanar gizo

Ya ce ziyarar ta ba zata a Ikoyi ita ce ta tabbatar da zargin da ake yi wa jami’an ofisoshin shige da fice na jihar Legas da suka hada da Ikoyi, Ikeja da garin FESTAC.

Asali: Legit.ng

Online view pixel