Jerin mutane 6 da ke da hannu a yawaitar magudin jarrabawa a Arewacin Najeriya, Prof. Salisu Shehu

Jerin mutane 6 da ke da hannu a yawaitar magudin jarrabawa a Arewacin Najeriya, Prof. Salisu Shehu

  • Shugaban jami'a a jihar Kano ya bayyana wasu matsalolin da suka jawo yawaitar satar jarrabawa a Arewa
  • Ya bayyana wasu hanyoyi shida da su ne manyan dalilai da suka jefa al'ummar Arewa cikin yawaitar satar jarrabawa
  • Ya bayyana hake cikin wata tattaunawa da wakilin Legit.ng Hausa kan batutuwan da suka shafi ilimi

Kano - Farfesa Salisu Shehu, kwararre a fannin ilimin shari'a kuma shugaban jami'ar Al-Istiqama da ke Sumaila a jihar Kano ya bayyana tushen matsalar magudin jarrabawa a kamarantun Arewacin Najeriya.

Farfesa ya bayyana hake yayin wata hira da wakilinmu na Legit.ng Hausa a farkon makon nan, inda ya bude maganganu da yawa da suke da alaka da karantarwa da ma harkar tabarbarewar ilimi a yankin Arewa.

Read also

An kama ma’aurata kan kashe dansu tare da binne shi cikin sirri saboda ‘rashin ji’

A cikin hirar, wakilinmu ya masa tambaya kan asalin musabbabin satar amsa a jarrabawar makarantu tare neman sanin a ina matsalar ta soma; shin bangaren malamai ne ko kuma hukumomi ko ma dai daliban.

Jerin mutane 6 da ke da hannu a yawaitar magudin jarrabawa a Arewacin Najeriya, Prof. Salisu Shehu
Shugaban Jami'ar Al-Istiqama, Farfesa Salisu Shehu | Hoto: Salisu Shehu
Source: Facebook

Jerin bangarori 6 masu hannu a wannan matsalar

Farfesa Salisu Shehu ya amsa tambayar da aka masa kan tushen matsalar satar amsa a makaranta, inda ya bayyana cewa:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Matsalar satar jarrabawa ba matsalace ta wani bangare guda ba. Dukkan al'umma tana da laifi game satar jarrabawa."

A bayanansa, ya danganta laifin satar jarrabawa ga wadannan bangarori guda shida kamar haka:

1. Gwamnati

Ya yi bayanin cewa, gwamnati ta gaza wajen ba da abubuwan da ake bukata don tabbatar da ingancin ilimi a kasar. Ya ce, wannan sakacin gwamnati ya faru ne ta hanyar rashin isassun kayayyakin aiki da kayayyakin karatu har ma dai da tabbatar da kwarewar malamai.

Read also

2023: Jiga-jigan PDP na Arewa sun dage kan tikitin takarar shugaban kasa

2. Hukumomin gwamnatin ilimi

A bangare guda, ya kuma bayyana hukumomin gwamnati da cewa suna tattare da son zuciya da rashawa wajen aiwatar da abubuwan da gwamnati ta samar wanda bai taka kara ya karya ba.

Ya kara da cewa:

"Sannan kuma su wadannan hukumomi saboda ba sa so gwamnati ta ga sun gaza, to suna taimakawa wajen a yi satar jarrabawa don nuna gwamnati cewa ana aiki ga jarrabawa tana yin kyau."

3. Shugabannin makarantu

A bangaren shugabannin makarantu, Farfesa ya bayyana cewa, rashin tsoron Allah da tsoron abin da ka iya biyo baya daga hukumomin ilimi na daya daga cikin dalilan yawaitar satar jarrabawa.

Hakazalika, ya lura da yadda shugabannin makarantu ke son farantawa hukumar ilimi ta hanyar kawo sakamakon jarrabawar dalibai mai kyau don samun daukaka sunan makarantarsu.

Ya ce:

"Don haka, idan ana cire tutar makarantu da 'Principals' din da jarrabawar makarantunsu ta fi kyau, duk da dai an san cewa ta hanyar satar jarrabawa suka samu, don haka wadanda suke kokarin su hanawa sai su ma su saki layi su ga cewa bai kamata kullum kowace shekara ake ganin makarantarsu ita ce ke ci baya ba."

Read also

Gobara ta yi kaca-kaca da Hedkwatar hukumar NPA, dukiyoyi sun kone kurmus

4. Malamai

Idan ana maganar matsalar harkar satar jarrabawa ta fannin malamai, Farfesa ya danganta laifin ga gwamnati, inda yace sam babu kwararrun malamai da suka cancanta kuma suka ishi a makarantu.

A kalaman Farfesa:

"Akwai gibi mai yawa wajen bukatar a samar da malamai; ba a samarwa. Sannan wadanda suke cikin harkar koyarwar basu da kwarewa ta azo a gani. To wannan shi ne yasa ya zamana babu kwarewar da za ta sa malami ya koyar yadda ya kamata."

5. Iyayen dalibai

Iyayen dalibai kuwa ya koka da rashin jin tsoron Allah da suke dashi tunda har za su iya amincewa a ba 'ya'yansu sakamakon jarrabawar da basu cancanta ba.

Game da gudunmawar iyaye a satar jarrabawa Farfesa ya ce:

"Sun san cewa ba jarrabawar ce ta hakika ba, amma sai mutum in ya ci jarrabawa ta hanyar karya ya zo yana tutiya wai yaronsa ya yi kokari ya samu 'Credits' 9 alhali ya san karya ne."

Read also

Garba Shehu: Saɓani tsakanin gwamnati da ɗan kwangila ne ya hana aikin wutar Mambila

6. Dalibai

A bangaren dalibai, Farfesa ya ce sun riga sun zama malalata kuma ba su da sha'awar karatu, inda ya koka da cewa dalibai a yanzu sun fi mayar da hankali kan wayoyin hannu da kafafen sada zumunta.

A ra'ayinsa, Farfesa ya lura cewa, amfani da wayoyin hannu da na'urorin sadarwa suna dauke hankalin dalibai wajenmayar da hankalinsu ga abin da zai amfane su na ilimi.

Ya kuma ce, kalle-kallen fina-finan Hausa a bangaren 'yan mata da kwallo a bangaren matasa maza sun ba da mummunar gudunmawa wajen kassara harkar ilimi tsakanin dalibai.

Abin kunya ne Najeriya ta ke kiran kanta uwa ga Afrika, inji tsohon sarkin Kano Sanusi II

A wnai labarin, Tsohon sarkin Kano, Muhammadu Sanusi ll, ya ce Najeriya ta rasa kimarta a matsayin uwa a Afirka ga sauran kasashen da suka bunkasa tattalin arzikin su, Daily Nigerian ta ruwaito.

Sanusi ya ce yanzu Najeriya tana bayan sauran wasu kasashen Afirka da yawa idan aka duba ta fuskar ci gaba.

Read also

Hasashe: Garabasa 4 da Shehu Sani kan iya samu ta dalilin komawa PDP

Sanusi wanda ya kasance Tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya, ya fadi haka ne a yayin rufe taron Babban Taron Zuba hannun Jari na Kaduna, mai taken, ‘KadInvest 6.0.’

Source: Legit.ng

Online view pixel