Karfin hali: Ƴan bindiga sun gargaɗi sojoji su fice daga wani gari a Filato domin za su kawo hari

Karfin hali: Ƴan bindiga sun gargaɗi sojoji su fice daga wani gari a Filato domin za su kawo hari

  • Wasu yan bindiga da ke neman kai hari a kauyen Miango da ke karamar hukumar Bassa a Filato sun gargadi sojoji da ke tsare garin
  • Maharan sun umurci sojojin su tattara kayansu su yi gaba idan ba haka ba kuma da su za su fara somman tabi kafin su shiga garin
  • Maharan sun dade suna kai wa manoman garin Miango hari kwanakin baya an yi sulhu amma kwatsam sai ga wasikar barazana

Plateau - Yan bindiga sun bukaci dakarun sojojin Nigeria su bar wuraren da suka kafa shinge a kusa da wani kauye a Miango, karamar hukumar Bassa a jihar Plateau.

A baya-bayan nan ne aka tura wasu sojoji zuwa yankin, bayan hare-haren da yan bindigan suke kai wa 'yan kauyen, The Cable ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Da duminsa: 'Yan sanda sun samo gawar basaraken da aka yi garkuwa da shi

Karfin hali: Ƴan bindiga sun umurci sojoji su fice daga wani gari a Filato domin za su kawo hari
'Yan bindiga sun umurci sojoji su fice daga wani gari a Filato domin za su kawo hari. Hoto: The Cable
Asali: Facebook

Sojojin da ke aiki karkashin Operation Safe Haven (OPSH), sun hana maharan kai wa yan kauyen hari.

Wasu masana kan lamarin sun shaidawa The Cable cewa maharan sun rubutawa yan kauyen wasika, suna umurtarsu da cewa su fada wa sojojin su tattara kayansu su bar inda suke domin za su kawo hari.

Daya daga cikin majiyoyin ya ce:

"Mun girke sojojin mu a wani wuri da ke tsakanin garuruwan biyu ne da kuma duwatsu domin ta wurin maharan ke zuwa.
"Sau da yawa, sun yi kokarin kutsawa cikin kauyen amma sojojin ke taka musu birki. A watan da ta gabata, mun yi musayar wuta da su mun rasa sojojin mu biyu.
"Kwanaki kadan da suka gabata, yan kauyen sun kawo wani wasika daga maharan da ke cewa sojojin su bar inda suke domin su samu daman kai hari, sunyi barazanar cewa idan sojojin basu tafi ba, su za a fara kaiwa hari."

Kara karanta wannan

Sabon hari: 'Yan bindiga sun kai hari masallaci, sun bindige masallata a jihar Neja

Majiyoyi daga rundunar soji ta ce tuni an sanar da hedkwatar sojoji abin da ke faruwa kuma ana shirin kawo karin sojoji don gudun ko ta kwana.

Mun yi kokarin sulhunta su

Wasu kwamandojin sojoji a yankin sun shaidawa The Cable cewa sun yi kokarin yin sulhu tsakanin yan kauyen da maharan.

Majiyoyi sun ce an gayyaci daya daga cikin shugabannin maharan a lokacin da aka kashe wasu manoma a gonakinsu.

Majiyar ya yi bayanin cewa maharan ba za su iya shigowa kauyen su kai hari ba saboda sojoji amma sojojin ba za su iya bin dukkan manoman zuwa gonakinsu su basu tsaro ba don haka suke nemi yin sulhu.

"Mun tuntube su, an yi sulhu cewa ba za su sake kai wa yan kauyen hari ba. An shafe a kalla makonni uku babu manomin da aka kai wa hari.
"Ganin wannan wasikar barazanar ya bada mamaki amma sojojin mu suna nan a cikin shiri kuma ba za mu bari su mamaye kauyen ba," - cewar majiyar.

Kara karanta wannan

Karin bayani: ISWAP ta hallaka wasu jiga-jigan kwamandojin Boko Haram da mabiyansu 18

Ba a samu ji ta bakin kakakin sojoji Onyema Nwachukwu ba game da lamarin.

Rahoto: Masu ƙera wa Boko Haram bama-bamai sun koma dazukan Kudancin Kaduna

A jiya, kun ji cewa shugabannin kungiyar Boko Haram da ke biyayya ga Bakoura Buduma sun mayar da masu hada musu bama-bamai dazukan yankin kudanci Kaduna, a cewar wani rahoton da PRNigeria ta fitar.

A baya-bayan nan ne aka mayar da masu hada bama-baman da ake kira Amaliyyah a tsakin 'yan ta'addan, zuwa Rijana, Igabi da Chikun a yankin kudancin Kaduna.

Majiyoyi daga ciki sun ce kungiyoyin biyu na Boko Haram za su yi amfani da duwatsun da ke yankin a matsayin mabuya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel