Da duminsa: 'Yan sanda sun samo gawar basaraken da aka yi garkuwa da shi

Da duminsa: 'Yan sanda sun samo gawar basaraken da aka yi garkuwa da shi

  • Bayan shekaru 2 da sace basarake a jihar Ribas, jami'an tsaro sun samo gawarsa a wani daji daure da itace
  • Dan mamacin mai suna Dr Doughlas, ya tabbatar da cewa sau biyu suna biyan kudin fansa domin a sako mahaifinsu
  • Ya ce a cikin watannin nan ne aka tabbatar musu da cewa an kashe shi, hakan yasa suka tsananta nema har aka samu gawar

Rivers - Rundunar 'yan sandan jihar Ribas ta samo gawar basarake mai shekaru sittin da daya wanda aka sace a shekarar 2019.

Jami'an 'yan sanda sun samo gawar Chief Robert Loolo ne a wasu yankuna da suka hada garuruwan Luwa, Bera da Bane, Daily Trust ta ruwaito.

Da duminsa: 'Yan sanda sun samo gawar basaraken da aka yi garkuwa da shi
Da duminsa: 'Yan sanda sun samo gawar basaraken da aka yi garkuwa da shi. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Daily Trust ta ruwaito cewa, har gida wasu matasa suka je inda suka tasa keyar Loolo a ranar 27 ga watan Yunin 2019.

Kara karanta wannan

Sabon hari: 'Yan bindiga sun kai hari masallaci, sun bindige masallata a jihar Neja

Dan mamacin mai suna Dr Douglas Fabeke, ya sanar da manema labarai cewa, sau biyu suna biyan kudin fansa domin samun kubutar da mahaifinsa daga hannun miyagun.

Ya ce an azabtar da basaraken kuma an daure shi a wani itace inda aka bar shi ya mutu kafin ya samu daukin jama'a.

"Wata kungiyar matasa ta je har gida, suka yi awon gaba da shi kan rikicin da suke yi na shugaban matasa. Mun yi kokarin rokon matasan su sako su, mun biya kudin fansa har sau biyu.
"Mun kai wa 'yan sanda da dukkan jami'an tsaron jihar korafi, sun shiga kuma sun yi kokarin ganin an sako shi amma shiru," dan shi ya tabbatar.
"Mun cigaba da bincike a watanni kadan da suka gabata, mun kama wani mai maganin gargajiya wanda ya ce an kashe shi sai dai bai san inda aka birne shi ba..

Kara karanta wannan

Yadda 'yan fashi suka harbi mai shagon POS saboda kin basu kudi cikin dadin rai

“Tun daga nan muka mayar da hankali inda a yau muka samo inda ya ke. Mun hadu tare da 'yan sandan Bori kuma mun shiga dajin.
“A nan muka gan shi a mace. Ana iya gane kamanninsa kuma mun fahimci an azabtar da shi. An daure shi a jikin bishiya ne," yace.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, SP Nnamdi Omoni, ya sanar da Daily Trust cewa jami'ansu sun samo gawar mamacin.

'Yan bindiga sun harbe sarakuna biyu har lahira a wurin taro

A wani labari na daban, masarautun gargajiya a jihar Imo sun shiga zaman makoki sakamakon kashe wasu sarakuna biyu da aka yi.

Daily Trust ta ruwaito cewa sarakunan biyu sun tafi hallartar taron masu ruwa da tsaki ne a Nnenasa, hedkwatar karamar hukumar Njaba na jihar a lokacin da bata garin suka kai hari.

Asali: Legit.ng

Online view pixel