Rahoto: Masu ƙera wa Boko Haram bama-bamai sun koma dazukan Kudancin Kaduna

Rahoto: Masu ƙera wa Boko Haram bama-bamai sun koma dazukan Kudancin Kaduna

  • Wani rahoto ya bayyana cewa an mayar da masu kera wa Boko Haram bama-bamai zuwa yankin Kudancin Kaduna
  • Hakan na zuwa ne a yayin da shugabannin ISIS ke shirin kawo wa kungiyar ISWAP ziyara a Afirka
  • A cewar majiyoyi daga masu tattara bayannan sirri, dalilin ziyarar shina zuwa basu horaswa da kawo musu kudade

Kaduna - Shugabannin kungiyar Boko Haram da ke biyayya ga Bakoura Buduma sun mayar da masu hada musu bama-bamai dazukan yankin kudanci Kaduna, a cewar wani rahoton da PRNigeria ta fitar.

A baya-bayan nan ne aka mayar da masu hada bama-baman da ake kira Amaliyyah a tsakin 'yan ta'addan, zuwa Rijana, Igabi da Chikun a yankin kudancin Kaduna.

Rahoto: Masu ƙera wa Boko Haram bama-bamai sun koma dazukan Kudancin Kaduna
Babura, bindigu da makamai da sojoji suka kwato hannun yan ta'adda yayin kwato Gwoza. Hoto: PRNigeria
Asali: Facebook

Majiyoyi daga ciki sun ce kungiyoyin biyu na Boko Haram za su yi amfani da duwatsun da ke yankin a matsayin mabuya.

Kara karanta wannan

Shugabacin Najeriya a 2023: Jerin kungiyoyi 20 da ke goyon bayan Tinubu a zabe mai zuwa

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A wani rahoton mai alaka da wannan, Kwamitin Shura na ISIS na shirin kawo wa shugabannin ISWAP ziyara, PRNigeria ta gano daga majiyoyin masu tattara bayannan sirri.

An gano cewa, Abu Ibrahim al-Hashimi al-Quraishi, shugaban ISIS ne ya bada umurnin kai ziyarar a kokarin da kungiyar ke yi domin sake yi wa kungiyar garambawul.

Majiyoyi sun shaidawa PRNigeria cewa dalilin ziyarar na ISIS shine bada horaswa da kudade domin a dauki sabbin mayaka a yankin Afrika bayan rasa mayakansu da dama.

Majiyar ta kara da cewa:

"Za kuma su hada kai da ISWAP domin yakar yan ta'addan Boko Haram masu yi wa Bakoura biyayya."

Jerin Sunaye: Shugabannin Ƴan Ta’adda da Ƴan Bindiga Da Aka Kashe Daga Farkon Shekarar 2021 Zuwa Yanzu

A wani rahoton, kun ji cewa duk da cewa har yanzu ba a kawo karshen yaki da ta'addanci ba a Nigeria, an samu wasu cigaba a shekarar 2021.

Kara karanta wannan

2023: Kungiyar Yarbawa ta tsaida ‘Dan takararta tilo a zaben Shugaban kasa daga APC

Kawo yanzu, an kashe a kalla shugabannin yan bindiga da yan ta'adda 12 a yayin da hukumomin tsaro ke cigaba da yaki da bata garin da ke adabar kasar.

Ga dai jerin sunayen shugabannin yan ta'addan da aka kashe a shekarar 2021 bisa sanarwar da rundunar sojojin Nigeria da rahotonni da sauran kafafen watsa labarai ke fitarwa.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel