An kuma: Sheikh Abduljabbar ya sake caccakar Laiyoyinsa a Kotu, ya nemi a bashi dama ya kare kansa

An kuma: Sheikh Abduljabbar ya sake caccakar Laiyoyinsa a Kotu, ya nemi a bashi dama ya kare kansa

  • Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara ya sake neman a bashi dama ya kare kansa saboda ya fahimci Lauyiyinsa ba zasu iya ba
  • A cewar shehin Malamin Lauyoyin na shi ba su da cikakkiyar kwarewa a ilimin addini, an yi taƙaddama a zaman kotun
  • Ɓangaren gwamnatin Kano sun sake gabatar da shaida ta biyu, wanda ya kasance ɗalibi ga malam Abduljabbar

Kano - An sake kallon wata dirama a babbar kotun shari'ar musulunci ta Kano, yayin da Sheikh Abduljabbar Kabara, ya sake neman a ba shi dama ya kare kansa.

Dailytrust ta rahoto cewa Shehin malamin ya sake sa'in sa da lauyoyin dake kokarin karesa a shari'ar da ake masa kan zargin batanci.

Tun farkon lokacin da gwamnatin Kano ta gurfanar da shi a gaban Kotu, Malamin ya ƙalubalanci lauyoyinsa da zarginsu, wanda ya tilasta musu aje aikin.

Kara karanta wannan

Yan sanda sun damke wani mutumi kan laifin turawa matar aure sakon "Inakwana Baby"

Sheikh Abduljabbar
An kuma: Sheikh Abduljabbar ya sake caccakar Laiyoyinsa a Kotu, ya nemi a bashi dama ya kare kansa Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

A ranar Alhamis, Malamin wanda ake zargi da batanci ga Manzon Allah (SAW), laifin da hukuncinsa kisa ne a addinin musulunci, yace shi bai yarda da lauyoyinsa ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewarsa, lauyoyin ba su da cikakken ilimin addinin musulunci sosai, don haka a bashi dama ya kare kansa.

Shin ɓangaren gwamnati ya sake gabatar da shaida?

A zaman kotun na yau, Lauyan ɓangaren masu shigar da ƙara, ya gabatar da shaidarsa ta biyu, wani mutumi mai suna Murtala Kabir Muhammad.

Murtala mazaunin Kofar Na’isa Lokon Makera ya bayyana wa kotu cewa shi ɗalibin sheikh Abduljabbar ne.

Yayin da aka nemi ko ɓangaren da ake ƙara suna da tambayoyi ga shaidan, lauyan Albduljabbar ya bayyana wa kotu cewa wanda yake kare wa yana son a bashi dama ya kare kansa.

Barista Muhamamd Amin Kabir, ya kafa hujja da sashi na 36 (6d) na kundin mulkin Najeriya wanda aka yi wa garambawul.

Kara karanta wannan

Yan siyasan Najeriya ne suke rura wutar rikici a Jos, Shugaban gwamnonin Arewa

Wane mataki Alƙali ya ɗauka?

A hukuncin da ya yanke kan haka, alƙalin kotun, Mai shari'a Ibrahim Sarki Yola, yace ɓangaren da ake ƙara suna da damar zaɓen wanda zai kare, ko wanda ake ƙara ya kare kansa ko kuma tawagar lauyoyinsa su kare shi.

Nan yake shehin malamin ya zaɓi a barshi ya kare kan shi, amma Lauyoyin sun jaddada cewa zasu cigaba da halartar shari'an har zuwa ƙarshe.

Ɓangaren lauyoyin gwamnati sun bayyana cewa duk da Malamin ya nemi ya rinƙa kare kansa, amma ya zama wajibi sai yana da Lauyoyi a shari'ar.

Bayan sauraron dukkan ƙorafe-korafen ɓangarorin biyu, Alkalin ya ɗage zaman har zuwa 11 ga watan Nuwamba 2021, kamar yadda Aminiya Hausa ta ruwaito.

Me shaidar da gwamnati ta gabatar ya bayyana?

Tun a farko dai, Murtala ya bayyana cewa ya ji Malam Abduljabbar yana faɗin maganganu marasa daɗi akan Annabi (SAW) kuma a lokuta da dama.

Kara karanta wannan

CAN ga FG: Ya kamata a garkame Sheikh Gumi saboda yiyuwar alaka da 'yan bindiga

Yace:

"A ranar 10 ga watan Augusta, na je masallacin da malam Abduljabbar yake karatu (Ashabulkhahfi) kuma na ji da kunne na ya na faɗin magana mara daɗi kan auren Annabi Muhammad da Nana Safiyya."
"Hakanan a ranar 20 ga watan Disamba, 2019 na ji Sheikh Abduljabbar yana batanci ga Annabi Muhammad (SAW)."

A zaman da ya gabata kafin wannan an samu ɓarkewar rikici tsakanin Malam Abduljabbar Kabara da Lauyoyinsa.

Shekih Abduljabbar ya zargi lauyan nasa da kin kare shi da kuma hana shi ya kare kansa a gaban kotu, musamman tambayoyi ga shaidu

Daga ƙarshe dai sai da Alkali ya baiwa kowa hakuri tsakaninsu, sannan aka cigaba da shari'an kuma daga ƙarshe aka ɗage zaman zuwa yau 28 ga watan Oktoba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel