Zargin batanci: Rikici ya barke tsakanin Sheikh AbdulJabbar Kabara da Lauyoyinsa a Zaman Kotu

Zargin batanci: Rikici ya barke tsakanin Sheikh AbdulJabbar Kabara da Lauyoyinsa a Zaman Kotu

  • Rahotanni daga kotun shari'ar musulunci ta jihar Kano sun bayyana cewa rikici ya ɓarke tsakanin Malam Abduljabbar da Lauyansa
  • Shekih Abduljabbar ya zargi lauyan nasa da kin kare shi da kuma hana shi ya kare kansa a gaban kotu
  • Daga ƙarshe dai sai da Alkali ya baiwa kowa hakuri tsakaninsu, sannan ya ɗage ƙarar zuwa 28 ga watan Oktoba

Kano - Rikici ya barke a kotun shari'ar musulunci ta jihar Kano yayin da Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara ya nuna rashin jin daɗinsa kan yadda lauyoyinsa basu kare shi a gaban kotu.

A karo na biyu shehin malamin ya zargi lauyoyinsa da rashin kareshi idan ana kawo shaida kuma basu ba shi dama ya kare kanshi.

Rahoton Dailytrust ya nuna cewa Malam Abduljabbar ya roki kotu ta bashi dama ya kare kansa tunda lauyoyinsa basu iyawa.

Kara karanta wannan

Shekara daya da rabi da Shugaba Buhari ya yi magana, har yau umarninsa bai fara aiki ba

Sheikh AbdulJabbar Kabara
Zargin batanci: Rikici ya barke tsakanin Sheikh AbdulJabbar Kabara da Lauyoyinsa a Zaman Kotu Hoto: dailynigerian.com
Asali: UGC

Mai sharia Ibrahim Sarki Yola, ya yi watsi da bukatar malamin, inda ya koma kan lauyansa, Umar Mohammed, wanda ransa ya baci bisa abinda wanda yake karewa ya yi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Gwamnati ta gabatar da shaidu

Tun da farko, a zaman kotun na yau Alhamis, lauyan gwamnati, Farfesa Mamman Lawan Yusufari (SAN), ya gabatar da shaidarsa ta farko.

Lauyan ya gabatar da wani mai suna, Adamu Muhammad, mai sana'ar ɗinki a Gwale, wanda ya tabbatar da cewa shi ɗalibinsa ne mai bibiyar karatunsa.

Adamu ya shaidawa kotu cewa ba ɗaya ba kuma ba biyu ba yaji Sheikh AbdulJabbar yana kalamai marasa daɗi ga Manzon Allah (SAW).

Adamu yace:

"Ranar 10 ga watan Agusta, 2019, naje masallacin da yake karatu na Asshabulkhahfi, da kunne na, na ji yana batanci ga Annabi Muhammad (SAW) a kan aurensa da Nana Safiyya (RA)."

Kara karanta wannan

Yadda 'Ruwa mai tsarki' ya raba Mata da Miji da suka shekara 10 suna gina soyayya

A yanke mun hukuncin kisa - AbdulJabbar

Freedon Radio ta rahoto cewa ana cikin sauraron shaidar ne Malam Abduljabbar ya ta shi yana mai cewa kamata ya yi a yanke mai hukuncin kisa.

A cewar Shehin Malamin da ace ana zarginsa da cin mutuncin Manzon Allah (SAW) to gara a kashe shi kowa ya huta.

Ya kuma kara da cewa tun a baya ya nemi lauyoyinsa su ba shi dama ya nuna inda maganganun da yake faɗa suke a cikin litattafan Hadithi amma suka ƙi.

Abu ya koma kamar wasan kwaikwayo

Abduljabbar yace lauyoyinsa ba su masa adalci domin sun hana shi kare kanshi sannan kuma basu yin kokarin kare shi.

Ana cikin hakane sai lauyansa, Barista Umar Muhammad ya katse shi da cewa Malamin ya ɗauka kamar a kasuwa yake, inda zai iya faɗin abinda ransa ya so.

Ya kara da cewa yasan cewa wannan shari'ar tana da hatsari sosai amma ya amsa, sai ga shi ba abinda malamin zai saka masa da shi sai zargi

Kara karanta wannan

Tsoho mai shekaru 60 ya kashe ɗansa mai shekaru 32 saboda saɓani da ya shiga tsakaninsu

Alkali ya ɗage sauraron ƙara

Da rikicin ya nemi yin ƙamari ne, Alkali Yola ya baiwa Shehin Malamin tare da lauyan nasa hakuri, sannan ya umarci Abduljabbar ya daina magana sai an nemi ya yi domin nan a kotu yake.

Daga nan sai mai shari'a ya ɗage zaman har dai 28 ga watan Oktoba, za'a dawo domin cigaba da sauraron sheda ta biyu.

A wani labarin kuma Majalisar Malaman Kano ta dakatar da Sheikh Khalil daga shugabanci saboda abu biyu

Majalisar malaman addinin musulunci ta jihar Kano ta dakatar da shugabanta, Sheikh Ibrahim Khalil daga shugabanci.

Majalisar da ta haɗa malaman Izala, Tijjaniyya da Kadiriyya, ta amince da ɗaukar wannan matakin ne saboda abu ɗaya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel