Yan siyasa ne suke rura wutar rikici a Jos, Shugaban gwamnonin Arewa

Yan siyasa ne suke rura wutar rikici a Jos, Shugaban gwamnonin Arewa

  • Gwamnan jihar Filato, Simon Lalong, ya zargi yan siyasar ƙasar nan da rura wutar rikici a jiharsa maimakon taimaka wa a warware ta
  • Lalong yace sunan da ake wa Filato lakabi da shi, shine gidan zaman lafiya da wurin shakatawa, amma yan siyasa sun bata komai
  • A cewar gwamnan, takwarorinsa na Arewa suna goyon bayan kirkiran yan sandan jiha domin kawo ƙarshe ƙalubalen tsaro

Plateau - Shugaban ƙungiyar gwamnonin Arewa kuma gwamnan Filato, Simon Lalong, ya zargi yan siyasa da ƙara rura wutar rikici a jiharsa.

Gwamnan ya faɗi haka ne a wurin taron kwana biyu kan tattalin arziki, wanda ya gudana a babban birnin tarayya Abuja.

Channels tv ta rahoto cewa taron ya maida hankali ne kan tsaron ƙasa, Ilimi da kuma siyasar Najeriya.

Kara karanta wannan

Saraki ya yi magana kan kudirin tsayawa takarar shugaban kasa a 2023 da shirin sauya sheka daga PDP

Gwamna Simon Lalong
Yan siyasa ne suke rura wutar rikici a Jos, Shugaban gwamnonin Arewa Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

A cewarsa an san jihar Filato da zaman lafiya kafin wasu yan siyasa su shigo su lalata lamarin saboda wata bukata ta ƙashin kansu.

Geamnan yace:

"Taken da ake wa jihar Filato shine jihar zaman lafiya da shaƙatawa, amma yanzun meke faruwa? Zan iya cewa yan siyasa ne suka fara taka rawarsu (A rikicin)."
"Mutane na kawo rikicin ƙabilanci, da addini a tsakaninmu, shiyasa yanzun mun fara kallon junan mu a matsayin abokan faɗa."
"Idan ni kirista ne bana son inga musulmi ya kusance ni, haka idan ni ɗan wannan ƙabila ne, bana son ɗan wata kabila ya zo wurina."

Arewa na goyon bayan yan sandan jiha - Lalong

Gwamnan Lalong ya bayyana cewa jihohin Arewa 19 na goyon bayan kafa yan sandan jiha domin daƙile kalubalen tsaron da ake fama da shi.

Kara karanta wannan

Ni zan karbi mulkin Najeriya daga hannun shugaba Buhari a 2023, Gwamna

Lalong ya zargi gwamnatocin da suka shuɗe a jihar da kara ingiza rikicin, maimakon nemo hanyoyin kawo ƙarshen sa, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Gwamnan yace abubuwan da suka jawo kashe mutane a jihar Filato, yasa gwamnatin jiha ta nemi shawarwari ga shugaba Buhari, da kuma shaida masa halin da ake ciki.

A wani labarin kuma Saraki ya yi magana kan kudirin tsayawa takarar shugaban kasa a 2023 da shirin sauya sheka daga PDP

Tsohon gwamnan jihar Kwara, Sanata Abubakar Bukola Saraki, yace yanzun ba ya tunanin kansa a siyasar Najeriya.

Saraki yace a halin yanzun fatan sa shine PDP ta shawo kan matsalolinta, ta zama tsintsiya ɗaya domin ceto Najeriya daga hannun APC.

Asali: Legit.ng

Online view pixel