Lantarki ta hallaka wani matashi yayin da yake satar wayoyin wuta a Kano

Lantarki ta hallaka wani matashi yayin da yake satar wayoyin wuta a Kano

  • Wani barawon wayoyin wutar lantarki ya gamu da ajalinsa a cikin transforma a jihar Kano
  • Lamarin ya afku ne a safiyar ranar Laraba lokacin da matashin da mukarrabansa suka far ma harabar kamfanin wutar da ke hanyar Dawanau – Dawakin Tofa
  • Mukarraban nasa sun tsere bayan faruwar lamarin inda suka bar gawarsa a jikin wutar

Jihar Kano - Wutar lantarki ta kashe wani mutumi da ba a san ko wanene ba yayin da yake satar wayoyin wuta daga transforma mallakin kamfanin wuta ta Kano (KEDCO).

Mummunan al’amarin ya faru ne a safiyar ranar Laraba, 27 ga watan Oktoba, lokacin da mutumin tare da mukarrabansa suka kai mamaya harabar kamfanin lantarkin da ke hanyar Dawanau – Dawakin Tofa a wajen garin Kano.

Kara karanta wannan

Kogi: 'Yan bindiga sun sheke rayuka 6, sun babbaka fadar Sarki da wasu gidaje masu yawa

Lantarki ta hallaka wani matashi yayin da yake satar wayoyin wuta a Kano
Lantarki ta hallaka wani matashi yayin da yake satar wayoyin wuta a Kano Hoto: vanguardngr.com
Asali: Facebook

Shugaban sashin sadarwa na kamfanin, Ibrahim Shawai, ya tabbatar da faruwar lamarin, jaridar Vanguard ta ruwaito.

Shawai ya ce barawon wayoyin ya taki rashin sa'a lokacin da aka dawo da wutar lantarki a transfoman.

Kakakin kamfanin lantarkin ya kuma koka da ayyukan masu sace-sacen wayoyin transfoma wanda ya ce suna yawan satar kayayyakin ma'aikatar.

Shawai ya ce:

"Ina addu'an Allah ya sa wannan ya zama izina ga sauran wadanda ke da dabi'ar sace-sacen kayanmu da na ma'aikatar."

Da aka tuntube shi, kakakin yan sandan jihar Kano, DSP Haruna Kiwaya, ya ce suna kan binciken lamarin, rahoton Daily Post.

Tashin hankali: Wayoyin wuta sun lantarke masu ibada ana tsaka da ayyukan Bauta a Lagos

A wani labari na daban, mun kawo a baya cewa mutane sun shiga tashin hankali da bala'i a cocin El-Adonai Evangelical dake Abule-Egba jihar Lagos, lokacin da wayoyin wutar lantarki suka faɗo kan mutane ana tsaka da ibada, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Sabon hari: 'Yan bindiga sun kai hari masallaci, sun bindige masallata a jihar Neja

Rahoto ya nuna cewa wutar da janye mutum biyu maza matasa da kuma yara mata biyu.

Wani shaida, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya shaidawa jaridar Dailytrust cewa lamarin ya auku ne yayin da mambobin cocin ke kokarin gyara tuta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel