Tashin hankali: Wayoyin wuta sun lantarke masu ibada ana tsaka da ayyukan Bauta a Lagos
- Mutane sun shiga tashin hankali yayin da wayoyin wutar lantarki suka faɗo a wata coci dake jihar Lagos
- Wayoyin wutar sun lantarke wasu daga cikin masu ibada a cocin El-Adonai Evangelical dake Abule-Egba
- Hukumar rarraba hasken wutar lantarki ta Ikeja, ta tabbatar da lamarin, tace tuni ta datse hanyar wutar yankin
Lagos - Mutane sun shiga tashin hankali da bala'i a cocin El-Adonai Evangelical dake Abule-Egba jihar Lagos, lokacin da wayoyin wutar lantarki suka faɗo kan mutane ana tsaka da ibada, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.
Rahoto ya nuna cewa wutar da janye mutum biyu maza matasa da kuma yara mata biyu.
Wani shaida, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya shaidawa jaridar Dailytrust cewa lamarin ya auku ne yayin da mambobin cocin ke kokarin gyara tuta.
Me ya haɗa tutar coci da wayoyin lantarki?
Wutar lantarkin ta lantarke mambobin cocin ne yayin da suke gyara domin baiwa shugabannin su damar shiga harabar cocin.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Legit.ng Hausa ta gano cewa fol ɗin da tutar cocin ke jiki ce ta taɓa wayar wutar lantarkin, wanda ya haddasa faruwar lamarin.
Sai dai har zuwa yanzun, ba'a gano cikakken bayanan waɗanda lamarin ya shafa ba.
Jami'an kwana-kwana sun kai ɗauki
An kira jami'an hukumar kashe wuta domin dakile lamarin, wanda ka iya haddasa rasa rayuwa da kuma asarar dukiyoyi.
Daraktan hukumar ta jihar Lagos, Mrs. Adeseye Margaret, wacce ta tabbatar da faruwar lamarin, tace wasu daga cikin waɗanda abun ya shafa sun sume a halin da ake ciki.
"Hukumar raba wutar lantarki dake Ikeja ta samu rahoto kuma nan take ta katse hanyar wutar yankin da abun ya faru, yayin da aka cigaba da ayyukan ceto."
A wani labari na daban kuma Sarkin Zazzau, Alhaji Ahmad Bamalli, ya nuna damuwarsa game da halin matsalar tsaro da yankin Arewa ke ciki
Sarkin yace ya zama wajibi yan Najeriya su cigaba da tallafawa kokarin gwamnati na kawo ƙarshen matsalar.
Bamalli ya yi godiya ga Allah (SWT) da ya ba shi ikon zama sarkin Zazzau, ba don wani karfi ko dabararsa ba.
Asali: Legit.ng