Shugaban Marasa Ji Marlians na cigaba da gurfana a kotu kan zargin damfarar yanar gizo

Shugaban Marasa Ji Marlians na cigaba da gurfana a kotu kan zargin damfarar yanar gizo

  • Hukumar EFCC ta gabatar da shaidu kan Naira Marley gaban kotun tarayya dake zamanta a jihar Legas
  • A cewar Shaidar, an samu hujjoji dake tabbatar da zargin da hukumar yaki da rashawa ke masa na zamba
  • Tun shekarar 2019 aka fara gurfanar da Naira Marley gaban kotu bayan damkeshi da hukumar EFCC tayi

Legas - A ranar Talata, an cigaba da gurfanar da Shahrarren mawaki kuma jagoran marasa ji na Najeriya, Afeez Fashola, wanda akafi sani da Naira Marley, gaban kotu.

Naira Marley ya gurfana ne gaban Alkali Nicholas Oweibo na babban kotun tarayya dake Ikoyi, jihar Legas, rahoton ChannelsTV.

A gurfanar da shi da akayi ranar Talata, hukumar hana almundahana EFCC ta gabatar da masanin ilmin binciken zaman watau Forensics, Anosike, a matsayin shaida kan karar da ta shigar kan Naira Marley.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari ta lashi takobin tsamo ‘yan Najeriya miliyan 2 daga jahilci duk shekara

Anosike ya bayyanawa Alkalin cewa an samu lambbobin katunan ATM da dama cikin wayar Naira Marley.

Masanin ya bayyana cewa sakonnin WhatsApp 2,410 wanda ke nuna yadda mawakin ya samu na lambobin katin ATM na mutane daban-daban.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Shugaban Marasa Ji Marlians na cigaba da gurfana kotu kan zargin damfarar yanar gizo
Shugaban Marasa Ji Marlians na cigaba da gurfana kotu kan zargin damfarar yanar gizo
Asali: Instagram

Yayinda aka tambayesa kan abin da ya gani, Anosike yace an samu sakonnin SMS 977 da kuma tattaunawa 1,433.

Bayan haka, ya yi bayanin cewa an turo lambobin katin mutane da dama da lokutansu da kuma OTP da aka samu a cikin wayarsa.

Daga karshe Alkalin ta dage karar zuwa ranar Laraba don kallon hujjojin a TV (Projector).

Laifin me Naira Marley yayi

Hukumar EFCC ta fara gurfanar da Naira Marley ne ranar 20 ga Mayu, 2019, kan zargin laifuka 11 wanda suka hada mallakar katunan ATM, da kuma zamba.

Naira Marley dai ya musanta zargin da ake masa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel