Yadda shugaba a NIS ya yi shigan burtu ya kame jami'ansa dumu-dumu da rashawa

Yadda shugaba a NIS ya yi shigan burtu ya kame jami'ansa dumu-dumu da rashawa

  • Mukaddashin Kwanturola na hukumar shige da fice ta kasa ya kame jami'ansa na aikata karbar rashawa
  • Ya bayyana cewa, ya dura ofishinsu, inda suka nemi ya biya makudan kudade ba bisa ka'ida ba
  • Ya bayyana cewa, gani ya kori ji, domin kuwa ya tabbatar da zargin da ake yi wa jami'an hukumar

Mukaddashin Kwanturola Janar na Hukumar Kula da Shige da Fice ta Najeriya (NIS), Isa Jere Idris, ya cafke wasu jami’an hukumarsa dumu-dumu a kokarinsu na hada harkallar badakala.

Idris wanda ya yi shigar burtu a matsayin mai neman fasfo na kasa da kasa a a ofishin rundunar da kejihar Legas, ya kama su lokacin da suka yi masa tayin taimaka masa wajen siyan fasfo din ta hanyar da bata dace ba.

Kara karanta wannan

Ba guduwa zan yi ba: Sheikh Zakzaky ya zargi gwamnatin Buhari da hana shi sakat

Shugaban hukumar NIS ya yi shigan burtu, ya kama jami'ansa da aikata badakala
Fasfo din Najeriya na ECOWAS | Hoto: nigerianinfopedia.com.ng
Asali: UGC

Mukaddashin Kwanturolan ya bayyana haka ne a wata hira da ya yi da jaridar Premium Times.

Ya ce ziyarar ta ba zata a Ikoyi ita ce ta tabbatar da zargin da ake yi wa jami’an ofisoshin shige da fice na jihar Legas da suka hada da Ikoyi, Ikeja da garin FESTAC.

Ya ce lokacin da ya tuntubi jami'an a ofishin na Ikoyi, an ba shi farashi daban-daban na fasfo.

Ya shaida wa Premium Times cewa:

“Lokacin da na tunkari jami’an, sun ba ni jadawalin farashi ba tare da sun gane ni ba. Sun ce fasfo mai shafuka 32 na tsawon shekaru biyar zan kashe N45,000 maimakon N27,000.
"Sun ce mai shafuka 64 na shekaru biyar zan kashe N55,000 maimakon N37,000, da N95,000 ga fasfo mai shafuka 64 na shekaru 10 maimakon N72,000.

Kara karanta wannan

An yanke wa Salisu ɗaurin gidan yari kan satar tukwane da kujeru a coci a Legas

“An tambaye ni daga ina na ce Jihar Neja. Sun kuma tambaye ni idan ina da shaidar zama dan kasa da sauran takardu kuma na ce ba ni da daya. Don haka suka ce za su karbi Naira dubu uku da dari biyar domin su samar min da dukkan takardun.”

Duk da haka, ya ce har yanzu jami'an ba su san ko wanene shi ba, kuma kwanturolan hukumar na Legas, Bauchi Aliyu, ya yi mamakin lokacin da ya bayyana a ofishinsa.

NAF ta karyata rahoton biyan 'yan bindiga N20m don kada su harbo jirgin Buhari

A baya kuwa, jaridar Punch ta ruwaito cewa, rundunar sojin saman Najeriya ta yi watsi da jita-jita da wasu ke yadawa a kafafen sada zumunta cewa, an biya 'yan bindiga N20m domin su mika wata bindigar harbo jirgin yaki ga gwamnati.

A yau ne aka samu rahoton da ke yawo a kafafen sada zumunta, wanda ke cewa, gwamnatin Buhari tare da sojojin saman Najeriya sun ba 'yan bindiga N20m a jihar Katsina domin su mika makamin harbo bindiga mallakarsu.

Kara karanta wannan

Da gaske Buhari Jibril ne na Sudan? A karshe Femi Adesina ya fayyace gaskiya

Jaridar Wall Street Journal ta bayyana a cikin wani rahoto a ranar Lahadi cewa NAF ta kulla yarjejeniyar ne yayin da Shugaban kasa, Manjo Janar Muhammadu Buhari (mai ritaya), ke shirin tafiya Katsina, jiharsa ta haihuwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel