Osinbajo na jagorantar zaman majalisar zartarwa yayin da Shugaba Buhari ke Saudiyya

Osinbajo na jagorantar zaman majalisar zartarwa yayin da Shugaba Buhari ke Saudiyya

  • A daidai lokacin da shugaba Muhammadu Buhari ke halartan wani taro a kasar Saudiyya, mataimakin shugaban kasa Osinbajo ya jagoranci zaman majalisar zartarwa
  • Osinbajo na shugabantar taron ne a dakin taro na ofishin uwargidar shugaban kasa, Abuja
  • Ministoci da manyan jami'an gwamnati duk sun hallara kai tsaye da kuma ta yanar gizo

Fadar shugaban kasa, Abuja - A yanzu haka, mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, na jagorantar zaman majalisar zartarwa a dakin taro na ofishin uwargidar shugaban kasa, Abuja.

Osinbajo na jagorantar zaman ne yayin da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ke birnin Riyadh, kasar Saudiyya domin halartan taron zuba jari, jaridar Punch ta rahoto.

Osinbajo na jagorantar zaman majalisar zartarwa yayin da Shugaba Buhari ke Saudiyya
Osinbajo na jagorantar zaman majalisar zartarwa yayin da Shugaba Buhari ke Saudiyya Hoto: Yemi Osinbajo
Source: Facebook

Wadanda suka halarci taron sun hada da babban sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, Ministan labarai da al'adu, Lai Mohammed da Atoni Janar na kuma ministan shari'a, Abubakar Malami.

Read also

Da dumi-dumi: Shugaba Buhari ya isa Saudiyya gabannin taron zuba jari

Sauran wadanda suka hallara sun hada da minitar kudi da tsare-tsaren kasa, Zainab Ahmed, Ministan ayyuka da gidaje, Babatunde Fashola, ministan sufurin jiragen sama, Hadi Sirika da kuma ministan lantarki, Abubakar Aliyu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Har ila yau, daga cikin wadanda suka hallara daga ofishoshinsu da ke Abuja ta yanar gizo akwai shugabar ma'aikatan tarayya, Folashade Yemi-Esan, da sauran ministoci, rahoton Channels TV.

Shugaba Buhari ya isa Saudiyya gabannin taron zuba jari

Legit.ng Hausa ta rahoto a baya cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya isa birnin Riyadh, kasar Saudiyya gabannin taron zuba jari a daren ranar Litinin, 25 ga watan Oktoba.

Bayan isarsu filin jirgin sama na Sarki Khalid, Shugaban kasar da tawagarsa sun samu tarba daga mataimakin gwamnan Riyadh, Yarima Mohammed bin Abdulrahman Abdulaziz.

Shugaba Buhari tare da sauran shugabannin duniya, za su halarci bude taron a ranar Talata, 26 ga watan Oktoba. Taron wanda zai shafe tsawon kwanaki uku zai mayar da hankali ne kan taken taron karo na 5 wato "Zuba jari a dan’adam".

Read also

Yanzu-Yanzu: Sojoji sun tsare Firayim ministan Sudan da wasu jiga-jigan gwamnatinsa

Source: Legit Nigeria

Online view pixel