Da dumi-dumi: Shugaba Buhari ya isa Saudiyya gabannin taron zuba jari

Da dumi-dumi: Shugaba Buhari ya isa Saudiyya gabannin taron zuba jari

  • Jirgin Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sauka a birnin Riyadh na kasar Saudiyya gabannin taron zuba jari
  • Shugaban kasar da mukarrabansa sun samu kyakkyawar tarba daga mataimakin gwamnan Riyadh, Yarima Mohammed bin Abdulrahman Abdulaziz
  • Za a bude taron ne wanda zai shafe tsawon kwana uku ne a ranar Talata, 26 ga watan Oktoba

Kasar Saudiyya - Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya isa birnin Riyadh, kasar Saudiyya gabannin taron zuba jari a daren ranar Litinin, 25 ga watan Oktoba.

Bayan isarsu filin jirgin sama na Sarki Khalid, Shugaban kasar da tawagarsa sun samu tarba daga mataimakin gwamnan Riyadh, Yarima Mohammed bin Abdulrahman Abdulaziz.

Da dumi-dumi: Shugaba Buhari ya isa Saudiyya gabannin taron zuba jari
Da dumi-dumi: Shugaba Buhari ya isa Saudiyya gabannin taron zuba jari Hoto: Femi Adesina
Asali: Facebook

Shugaba Buhari tare da sauran shugabannin duniya, za su halarci bude taron a ranar Talata, 26 ga watan Oktoba.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Shugaba Buhari zai tafi Saudiyya gobe Litinin taron zuba jari, kuma zai yi Umrah

Taron wanda zai shafe tsawon kwanaki uku zai mayar da hankali ne kan taken taron karo na 5 wato "Zuba jari a dan’adam".

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Mai Magana da yawun shugaban kasa, Mallam Garba Shehu ne ya sanar da hakan a wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na Facebook.

Shugaba Buhari zai tafi Saudiyya Litinin taron zuba jari, kuma zai yi Umrah

A baya mun kawo cewa Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, zai tafi kasar Saudiyya ranar Litnin, 25 ga watan Oktoba, 2021 domin halartan taron hannun jari sannan kuma yayi Ibadar Umrah.

Mai magana da yawunsa, Mallam Garba Shehu, ya bayyana hakan a jawabin da ya saki ranar Lahadi a shafinsa na Facebook.

A cewarsa, shugaban kasan zai gana da manyan yan kasuwan Najeriya, manajojin bankuna, masana ilmin makamashi da sauransu.

Kara karanta wannan

2023: Jihar Kano a shirye take ta goyi bayan burin Tinubu a shugabancin Najeriya, kakakin majalisa

Asali: Legit.ng

Online view pixel