Cin Bashi Don Ayyukan Cigaba Ba Laifi Bane: Cewar Bankin CBN

Cin Bashi Don Ayyukan Cigaba Ba Laifi Bane: Cewar Bankin CBN

  • Babban Dirakta a bankin CBN yace ko manyan kasashe irin Amurka na karban bashi don amfani
  • Diraktan ya yi kira ga yan Najeriya su daina zagin karban bashin da gwamnatin tarayya ke yi
  • A 2022, Najeriya ta biya bashi da dukkan kudaden shigan da ta samu na haraji

Edo - Babban bankin Najeriya (CBN) ya bayyana cewa karban bashi don gudanar da ayyukan cigaba ba laifi bane saboda kasashen da suka cigaba irinsu Amurka har yau suna cin bashi.

Shugaban sashen katabta dukiyoyin jingina na cin bashi watau National Collateral Registry (NCR) na bankin CBN, Mr Bulus Musa ya bayyana cewa yan Najeriya su daina sukan gwamnati don ta karbi bashi don yin ayyukan alfanu.

Ya jaddada cewa idan akayi amfani da basussukan yadda ya kamata, zai ciyar da kasar gaba.

Bulus Musa, wanda ya samu wakilcin Mataimakin Dirakta a CBN, Dr. Xavier-Itam Okon, ya yi jawabi ne a taron masu ruwa da tsaki a harkar noma da akayi a Benin, jihar Edo, rahoton TheNation.

Musa, ya bayyana cewa an kafa sashe katabta dukiyoyin jingina ne a 2015 don taimakawa kananan yan kasuwa wajen cin bashi tare yin amfani da dukiyoyinsu wajen jingina.

Bankin CBN
Cin Bashi Don Ayyukan Cigaba Ba Laifi Bane: Cewar Bankin CBN
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Muna Shawaran Sake Ciwo Bashi Daga Wajen Asusun Lamunin Duniya, Ministar Kudi

A wani labarin kuwa, Ministar Kudi da Kasafin Kudi, Zainab Ahmed Shamsuna, ta bayyana cewa gwamnatin tarayya na shawarar sake ciyo sabon bashi daga wajen asusun lamunin duniya watau IMF.

Zainab ta bayyana hakan yayin taron bankin duniya da IMF da ya gudana ranar Laraba a Washington, babbar birnin Amurka.

Ministar kudin ta kara da cewa ta dade tana tattaunawa da hukumomin kudi don ganin yadda baiwa Najeriya talala wajen biyan kudin basussukan da ake bin kasar.

Najeriya Na Zaman Tsammani Yayinda China Taci Kenya Tara Kan Rashin Biyan Bashi Kan Lokaci

A wani labarin kuwa, Gwamnatin kasar Sin ta bukaci kasar Kenya ta biyar tarar Sh1.312 billion(N4.71 billion) bisa jinkiri wajen biyan kudin bashin da ake binta.

Sin ta baiwa Kenya bashin kudaden ne don gina layin dogon jirgin kasa amma sun gaza samun isasshen kudin shiga don biyan bashin.

Jaridar BusinessDaily Kenya ta ruwaito cewa kasar ta karbi bashin rabin Tiriliyan na Shillings daga wajen Kasar China, don gina layin dogon Mombasa zuwa Naivasha.

Asali: Legit.ng

Online view pixel