Gwamnonin kudu sun gana a jihar Legas, Sun cimma matsaya kan abubuwa da dama

Gwamnonin kudu sun gana a jihar Legas, Sun cimma matsaya kan abubuwa da dama

  • Gwamnonin yankin kudu maso yamma sun gana da juna a gidan gwamnatin jihar Legas ranar Talata
  • A cewarsu abubuwan da suka tattauna suna da matukar muhimmanci kuma akwai bukatar sirri
  • Gwamnoni biyar daga cikin shida sun halarci taron, yayin da gwamnan Oyo ya tura mataimakinsa ya wakilce shi

Lagos - Mambobin ƙungiyar gwamnonin yankin kudu maso yamma sun gana a jihar Legas ranar Talata, domin tattaunawa a kan lamarin tsaro.

Punch ta rahoto cewa gwamnonin sun tattauna muhimman batutuwa wanda suka shafi matsalolin yankinsu, da kuma hanyar kawo cigaba.

Gwamnan Legas, Babajide Sanwo-Olu, shine ya karbi bakuncin takwarorinsa a gidan gwamnati, kwanaki uku kacal bayan harin da aka kai gidan yari a Ibadan.

Kudu maso yamma
Da Dumi-Dumi: Gwamnonin kudu sun gana a Legas, Sun bayyana matsayarsu kan tsaro Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Shin dukka gwamnonin sun halarta?

Gwamnoni biyar sun samu halartar taron, wanda aka fara shi da misalin ƙarfe 4:30 na yamma kuma cikin sirri.

Kara karanta wannan

Gwamna Zulum zai gwangwaje malaman makaranta da ƙarin Albashi a jihar Borno

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, shine bai samu halarta ba, amma ya turo mataimakinsa, Rauf Olaniyan, ya wakilce sa.

Me gwamnonin suka tattauna?

Da yake jawabi ga manema labarai, shugaban ƙungiyar gwamnonin kuma gwamnan Ondo, Rotimi Akeredolu, yace sun tattauna batutuwa da dama.

Gwamnan ya bayyana cewa a wani ɓangaren tattaunawar tasu sun yi mahawara kan yanayin tsaron da suke fama da shi a yankin.

Hakanan kuma yace sun tattauna akan kamfanin Oodua, wanda mallakin jihohin yankin kudu maso gabas ne baki ɗaya, amma ya ki sakin bayani saosai.

Ba mu son faɗa wa duniya abinda muka tattauna

Akeredolu ya ƙara da cewa ƙungiyarsu bata son fallasa duk abubuwan da suka tattauna domin suna bukatar sirri.

Gwamnan yace:

"Mu duka gwamnonin kudu maso yamma mun gana yau, kuma mun tattauna kan abubuwa da dama. Mun tattauna kan abun da ya haɗa mu baki ɗaya, wato kamfanin Oodua."

Kara karanta wannan

Mutum hudu sun mutu yayin da rikici ya barke tsakanin mutanen gari da fulani makiyaya a Kaduna

"Daga karshe mun cimma abubuwa da dama, waɗanda suka shafi tsaro, amma ba zami magnaar su anan ba."
"Kawai ina magana da ku ne dan tabbatar da cewa mun gana yau amma ba zamu fallasa abubuwan da muka cimma ba."

A wani labarin kuma Saraki ya yi magana kan kudirin tsayawa takarar shugaban kasa a 2023 da shirin sauya sheka daga PDP

Tsohon shuagaban majalisar dattijai, Sanata Bukola Saraki, yace a wurinsa baya kallon siyasa a bukatun karan kansa kaɗai.

Dailytrust tace Saraki ya faɗi haka ne yayin da yake bada amsa kan ko zai fice daga PDP matuƙar ba ta bashi tikitin tsayawa takarar shugaban ƙasa ba a 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel