Mutam uku sun mutu yayin da rikici ya barke tsakanin mutanen gari da fulani makiyaya a Kaduna

Mutam uku sun mutu yayin da rikici ya barke tsakanin mutanen gari da fulani makiyaya a Kaduna

  • Akalla mutum hudu sun mutu, wasu uku sun jikkata a wani rikici tsakanin makiyaya da mutanen gari a jihar Ƙaduna
  • Rahoto ya bayyana cewa lamarin ya auku ne kan hanyoyin da makiyaya ke wucewa da shanunsu a ƙaramar hukumar Zangon Kataf
  • Gwamnan jihar, Malam Nasiru El-Rufai, ya nuna alhinisa tare da kira ga jama'a su daina ɗaukar doka a hannunsu

Kaduna - Wani rikici da ya ɓarke tsakanin mutane da fulani makiyaya ya yi sanadin mutuwar mutum hudu, wasu da dama suka jikkata a Jankasa ƙaramar hukumar Zangon Kataf, jihar Kaduna.

Vanguard ta ruwaito cewa lamarin ya auku ne kan wuraren da fulani ke wucewa da shanunsu, wanda daga baya ya zama faɗa da makami a tsakaninsu.

Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida, Samuel Aruwan, shine ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun kutsa kai wurin Ibada ana tsaka da bauta, Sun yi awon gaba da mutum 3

Jihar Kaduna
Mutam hudu sun mutu yayin da rikici ya barke tsakanin mutanen gari da fulani makiyaya a Kaduna Hoto: Channesltv.com
Asali: UGC

Yace rahoton da jami'an tsaro suka baiwa gwamnati ya nuna cewa ɓangarorin biyu sun gwabza da juna kafin jami'ai su karaso kuma su shawo kan lamarin.

Me rikicin ya haifar?

Mista Aruwan yace bayan arangama tsakanin ɓangarorin biyu an gano cewa mutum huɗu sun mutu, Luka Nelson,Timothy Koni ,Pasi Peter amda George Frances.

Hakanan kuma wasu uku sun jikkata, waɗan da suka haɗa da Daniel Dauda, Extra James da Henry Frances, kuma an garzaya da su asibiti.

Wasu yan bindiga sun kaiwa Fulani hari

Hakanan kuma hukumomin tsaro a jihar sun tabbatar da cewa wasu yan bindiga sun farmaki Manchok, karamar hukumar Kaura.

Amma jami'an tsaro sun gano cewa an kai wannan harin ne domin ɗaukar fansa a kan rikicin da ya faru da farko.

Kara karanta wannan

Cikin mako ɗaya, Miyagun yan bindiga sun hallaka Sarakuna biyu da wasu mutum 45 a Najeriya

Gwamna ya nuna rashin jin daɗinsa

Da yake martani kan lamarin, gwamna El-Rufa'i ya nuna takaicinsa kan rikicin tare da addu'ar Allah ya jikan mamatan.

Gwamnan ya kuma yi kira ga mutanen yankin su rungumi doka su daina ɗaukar doka a hannun su, kamar yadda channels tv ta ruwaito.

A wani labarin kuma Gwamnonin Kudu sun bukaci shahararren malami a Najeriya ya daina caccakar Shugaba Buhari

Gwamnonin yankin kudu maso gabas sun roki shahararren malamin nan na addinin kirista, Rabaran Ejike Mbaka, ya daina magana mara ɗaɗi akan shugaban ƙasa Buhari.

Shugaban gwamnonin yankin, Gwamna David Umahi, tare da rakiyar gwamna Ifeanyi Ugwuanyi, na jihar Enugu , sune suka roki malamin amadadin sauran.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Tags:
Online view pixel