Katsina: Jami'an tsaro sun kai samame sansanonin 'yan bindiga, sun kwato dabbobi 102

Katsina: Jami'an tsaro sun kai samame sansanonin 'yan bindiga, sun kwato dabbobi 102

  • Jami'an rundunar hadin guiwa da suka hada da sojoji, 'yan sanda da 'yan sa kai sun kai farmaki sansanonin 'yan bindiga a Katsina
  • Jami'an tsaron sun dira a sansanin Bala wuta da ke Jibia tare da wani sansani a DutsinMa inda suka ragargaji 'yan bindiga
  • Sun yi nasarar kwato dabobin sata da suka hada da shanu, akuyoyi tare da tumaki da za su kai 102 daga sansanonin Mezegoji da Kadoji

Katsina - Ayyukan hadin guiwar jami'an tsaro a kananan hukumomin Jibia da DutsinMa na jihar Katsina a ranar Lahadi sun bankado sansanonin 'yan bindiga a jihar.

Bayan musayar wuta da aka yi tsakanin jami'an tsaron da 'yan bindigar, an samu ceto dabbobi dari da biyu daga wurin barayin.

Jami'an tsaron da suka hada da 'yan sanda, sojoji da kuma 'yan sa kai sun tsinkayi sansanonin 'yan bindiga da ke kauyukan Kadoji da Megezoji tare da ragargazar 'yan bindigan tare da kwato dabbobin satan.

Kara karanta wannan

An shiga halin fargaba a sansanin NYSC da ke Zamfara yayin da ‘yan bindiga suka sace masu yiwa kasa hidima

Katsina: Jami'an tsaro sun kai samame sansanonin 'yan bindiga, sun kwato dabbobi 102
Katsina: Jami'an tsaro sun kai samame sansanonin 'yan bindiga, sun kwato dabbobi 102. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar Katsina, SP Gambo Isah, ya tabbatar da aukuwar lamarin a ranar Litinin, jaridar The Punch ta ruwaito.

Ya yi bayanin cewa, sun kai farmakin ne bayan bayanai da suka samu na ayyukan 'yan ta'addan a kananan hukumomi biyun.

Isah ya ce, "A ranar Lahadi, 24 ga watan Oktoban 2021 tsakanin karfe 11 da rabi na safe zuwa karfe 1 da minti 15 na rana, dogaro da bayanan sirri, jami'an tsaron hadin guiwa da suka hada da 'yan sanda, sojoji da 'yan sa kai sun yi aiki a kauyen Kadoji da ke Jibia a wani sansanin dan bindiga mai suna Bala Wuta.
"Bayan gagarumar arangamar tare da musayar ruwan wuta, an fatattaki 'yan bindiga daga sansaninsu. Tawagar ta yi nasarar lalata sansanin tare da samo shanu 15, akuyoyi 28 da tumaki 12 da suka sace.

Kara karanta wannan

Yadda mawallafin ShaharaReporters ya sha duka a hannun 'yan daba a harabar kotun Abuja

"Hakazalika, a karamar hukumar Dutsinma, jami'an tsaro sun je har sansanin 'yan bindiga da Megezoji a dajin Yantumaki, sun fatattaki 'yan bindiga tare da tarwatsa sansanin. Sun samo shanu 28 tare da akuyoyi 19."

Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, Isah ya ce hukumar ta mayar da hankali wurin yaki da duk wasu tsagerun 'yan bindiga tare da shan alwashin kama su da maganinsu kamar yadda doka ta tanadar.

Gwamnatin Kaduna ta fallasa hanyoyi 6 da 'yan bindiga ke samun kudin shiga

A wani labari na daban, gwamnatin jihar Kaduna ta fallasa inda miyagun 'yan bindiga da suka addabi jihar ke samun kudaden shiga.

Daga cikin hanyoyin samun kudinsu kamar yadda gwamnatin jihar tace, shi ne wurin karbar kudin fansa daga 'yan uwan wadanda suka sace, Daily Trust ta ruwaito.

Wannan na kunshe ne a rahoton tsaro na watanni uku da kwamishinan tsaron cikin gida, Samuel Aruwan ya mika wa gwamnatin jihar kuma Daily Trust ta samu kwafi.

Kara karanta wannan

Rahoto: 'Yan bindiga sun sace sama da mutane 830 a jihar Kaduna cikin watanni 3

Asali: Legit.ng

Online view pixel