An shiga halin fargaba a sansanin NYSC da ke Zamfara yayin da ‘yan bindiga suka sace masu yiwa kasa hidima

An shiga halin fargaba a sansanin NYSC da ke Zamfara yayin da ‘yan bindiga suka sace masu yiwa kasa hidima

  • 'Yan bindiga sun yi awon gaba da wasu masu yiwa kasa hidima a hanyarsu ta zuwa sansanin NYSC da ke karamar hukumar Tsafe, jihar Zamfara
  • Har ila yau an tattaro cewa maharan sun tafi da wasu mutane a yayin harin bayan sun far wa motarsu mai lamba GBK 339 ZY wacce ta fito daga jihar Benue
  • Rundunar 'yan sandan jihar ta tabbatar da lamarin, ta kuma ce tuni jami'an hadin gwiwa suka kaddamar da aiki domin ceto wadanda aka sacen

Tsafe, jihar Zamfara - Yan bautar kasa sun shiga zullumi a jihar Zamfara biyo bayan sace wasu takwarorinsu da ‘yan bindiga suka yi a hanyarsu ta zuwa sansanin NYSC da ke karamar hukumar Tsafe.

Koda yake rundunar ‘yan sanda ta tabbatar da sace yan bautar kasar biyu a hanyar babban titin Sheme-Tsafe da ke jihar, shaidu sun ce har yanzu ba a ga wasu mutum shida ba bayan afkuwar lamarin a ranar Talata.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: ‘Yan bindiga sun yi garkuwa da yaya da kanwarta

An shiga halin fargaba a sansanin NYSC da ke Zamfara yayin da ‘yan bindiga suka sace masu yiwa kasa hidima
An shiga halin fargaba a sansanin NYSC da ke Zamfara yayin da ‘yan bindiga suka sace masu yiwa kasa hidima Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Sansanin yan bautar kasa na jihar Zamfara na a yankin Tsafe ne.

Rundunar ‘yan sandan ta ce an kaddamar da aikin bincike da ceto domin kubutar da yan bautar kasar da sauran mutanen da lamarin ya cika da su, Premium Times ta rahoto.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kakakin ‘yan sandan jihar, Muhammad Shehu, a cikin wata sanarwa, ya ce kwamishinan yan sanda a jihar, Ayuba Elkana ya ziyarci sansanin.

Elkana ya kuma ba Jami’an NYSC tabbacin samar da tsaro ga yan bautar kasa a sansanin, Vanguard ta kuma rahoto.

Sanarwar ta ce:

“Rahoton da rundunar yan sandan jihar Zamfara ta samu daga jagoran NYSC a jihar ya nuna cewa an sace yan bautar kasa biyu da aka turo jihohin Kebbi da Sokoto daga jihar Benue a hanyar Tsafe-Gusau tare da wasu mutane a ranar Talata, 19 ga watan Oktoba, 2021 da misalin karfe 2230.

Kara karanta wannan

Ana wata ga wata: ‘Yan bindiga sun cinna wuta a fadar sarkin Imo

"An samu rahoton a safiyar yau lokacin da kwamishinan yan sanda, CP Ayuba N. Elkana ya ziyarci sansanin yan bautar kasa a Tsafe domin duba yanayin tsaro a sansanin don tabbatar da tsaron yan bautar kasa.
“Idan za a tuna cewa a ranar 19 ga watan Oktoba, 2021, da misalin karfe 2230, yan bindiga sun tsare wata mota mai lamba GBK 339 ZY yayin da suke tafiya daga Benue zuwa jihar Sokoto kusa da kauyen Wanzamai a karamar hukumar Tsafe. Sakamakon haka, An sace fasinjoji wadanda ba a san ko su wanene ba.
“Kwamishinan yan sandan yayin da yake martani, y sanar da Shugaban NYSC din cewa rundunar ta fara bincike a cikin lamarin da nufin samo ainahin adadin yan bautar kasar da aka sace.
“Hakazalika, an fara aikin bincike da ceto don ganin an tsiratar da yan bautar kasar da sauran wadanda aka sace.
“Kwamishinan yan sandan, a jawabinsa zuwa ga yan yiwa kasa hidima, ya basu tabbacin cewa yan sanda Za su jajirce domin tsaron rayukan su sannan ya bukace su da kasance a ankare."

Kara karanta wannan

Sai mun hada kai ne za mu iya cin galaba a kan miyagu – APC kan harin jirgin kasa

Yadda aka sace wata budurwa bayan kammala digiri tana jiran shiga sansanin NYSC, kuma aka kashe ta a Makurdi

A gefe guda, wata budurwa yar kimanin shekara 24 wacce ta kammala karatun jarida a jami'ai jihar Benuwai, Joy Onoh, ta rasa ranta hannun wasu da ba'a gano su waye ba.

Dailytrust ta ruwaito cewa matashiyar ta rasa ranta ne a wani wuri da ake kira 'North Bank suburb' dake Makurdi, babban birnin jihar Benuwai.

Rahotanni sun bayyana cewa wasu mutane sun sace Joy ne bayan sun bukaci ta kai musu abubuwan da take siyarwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel