Yan bindiga sun hana mu sakat, suna kwashe abincin da muka noma a gonaki, Basarake a Katsina ya koka

Yan bindiga sun hana mu sakat, suna kwashe abincin da muka noma a gonaki, Basarake a Katsina ya koka

  • Hakimin karamar hukumar Batsari, Tukur Mu'azu Ruma, ya bayyana halin da mutanen Katsina ke ciki a hannun yan bindiga
  • Basaraken yace a halin yanzun yan ta'addan sun hana mutane sakat, ta hanyar kashe su da kuma hana su zuwa gonakinsu
  • A cewarsa yanzun yan bindiga ne suke kwashe abincin da mutane suka noma a gonaki

Katsina - Hakimin ƙaramar hukumar Batsari, (Sarkin-Ruman Katsina), a jihar Katsina, Tukur Mu’azu Ruma, yace yan bindiga na shigowa yankin daga jihar Zamfara.

Leadership ta rahoto Basaraken na kokawa kan yadda yan bindiga da suka tsero daga ruwan wutan Sojoji a Zamfara suka hana mutane sakat, kuma suke girbe abinda aka noma a gona.

A cewar Hakimin, wannan ruwan wutan da sojoji ke yi a kan yan bindiga, ya tilasta musu tserewa zuwa ƙananan ƙauyuka dake makotan jihohi.

Kara karanta wannan

Matsalar tsaro: Miyagun yan bindiga sun ƙone fadar basaraken gargajiya a Najeriya

Yan bindiga
Yan bindiga sun hana mu sakat, suna kwashe abincin da muka noma a gonaki, Basarake a Katsina ya koka Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Da yake zantawa da manema labarai a fadarsa dake Batsari, Hakimin yace yan bindigan sun hana mutane zuwa su girbo abinda suka noma a gonakinsu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Bugu da ƙari yace yan ta'addan na fatattakar mutanen ƙauyuka tare da kwashe kayayyakin abincin su, sannan su haɗa da na gonakinsu.

Shin matakan da gwamnati ta ɗauka suna aiki a Katsina?

Ruma ya ƙara da cewa yan bindigan da sojoji suka fatattaka daga jihar Zamfara, sune suke kafa sansani a dazukan iyaka da Katsina kamar dajin Runka da sauransu.

Yace:

"Sakamakon matakan tsaro da aka ɗauka kan yan bindiga, musamman datse hanyoyin sadarwa, yan bindigan suna shan wahala sabida haka suke harin kauyuka suna satar kayan abinci."
"Kwanan nan sun kai hari Yasore, inda suka kashe manoma 11 kuma suka ƙona gidajensu. Bayan harin kuma yan bindigan sun hana mutane zuwa gonakinsu."

Kara karanta wannan

Da duminsa: Yan bindiga sun sake kai hari ofishin yan sanda, sun saki fursunoni

"A halin yanzun yan bindigan ne suke kwashe kayan da mutane suka noma kamar Masara, Dawa, Gero da sauransu. Abin da takaici a kashe mutane kuma a hana su kwaso abinda suka noma."

Ina mafita?

Daga ƙarshe hakimin ya yi kira ga hukumomi su ƙara turo jami'an tsaro zuwa yankin domin magance ayyukan yan bindiga, kuma mutane su samu damar zuwa gonakinsu.

Ya kuma ƙara da cewa dokar tsaro da gwamna Aminu Bello Masari ya sanya wa hannu ta fara haifar da ɗa mai ido.

Yace gwamnatin Katsina ta ɗauki matakan yaƙi da ayyukan yan bindiga, ta hanyar datse sabis a ƙananan hukumomi 13.

A wani labarin kuma Wasu gwamnonin Arewa sun bada tallafin miliyan N20m ga iyalan mutanen da aka kashe a Sokoto

Gwamnonin arewa maso gabas ƙarƙashin ƙungiyarsu, sun bada tallafin miliyan N20m ga iyalan waɗanda harin kasuwar Goronyi ya shafa a Sokoto.

Legit.ng Hausa ta rahoto muku cewa a ranar 17 ga watan Oktoba, wasu miyagun yan bindiga suka buɗe wuta kan mai uwa da wabi a Kasuwar Goronyo, mutane da dama suka mutu.

Kara karanta wannan

Sarkin Birnin Gwari ya ce a yanzu 'yan fashi abinci suke nema maimakon kudin fansa

Asali: Legit.ng

Online view pixel