Da duminsa: Yan bindiga sun sake kai hari ofishin yan sanda, sun saki fursunoni

Da duminsa: Yan bindiga sun sake kai hari ofishin yan sanda, sun saki fursunoni

  • Yan bindiga da ake zargin IPOB ne na cigaba da kai hare-hare ofishohin yan sanda a Imo
  • Wannan ya biyo bayan kashe sarakunan gargajiya biyu da akayi a jihar
  • Yan bindiga sun kubutar da fursunonin dake tsare a ofishin yan sanda

Isiala Mbano LGA, Imo - Wasu yan bindiga da ake zargin yan ta'addan IPOB/ESN ne sun kuma kai hari ofishin yan sanda a inda suka banka wuta hedkwatar yan sandan karamar hukumar Isiala Mbano.

Punch ta ruwaito cewa yan bindigan sun kai hari ofishin dake unguwar Umuelemai ne yayinda ake ruwan sama cikin daren Alhamis, 21 ga Oktoba, 2021.

An tattaro cewa yan sandan dake wajen sun arce da kafafunsu yayinda yan bindigan suka bude musu wuta, riwayar Sahara Reporters.

A cewarta, wani mazaunin garin wanda ya bukaci a sakaye sunansa yace yan bindiga sun budewa ofishin wuta ratata.

Kara karanta wannan

Matsalar tsaro: Miyagun yan bindiga sun ƙone fadar basaraken gargajiya a Najeriya

A cewarsa:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Harbe-harben na da tashin hankali. Hankulanmu sun tashi sosai. Sai da suka tabbatar ofishin ta kone gaba daya kafin suka wuce."

Punch ta kara da cewa wani babban jami'in dan sanda ya tabbatar da harin kuma yace sun kaddamar da bincike kan lamarin.

Da duminsa: Yan bindiga sun sake kai hari ofishin yan sanda, sun saki fursunoni
Da duminsa: Yan bindiga sun sake kai hari ofishin yan sanda, sun saki fursunoni
Asali: UGC

Miyagun yan bindiga sun ƙone fadar basaraken gargajiya a Najeriya

Wasu tsagerun yan bindiga da ba'a gane ko suwaye ba sun ƙone fadar Dagacin Etekwuru dake ƙaramar hukumar Ohaji/Egbema, jihar Imo.

Punch ta rahoto cewa maharan sun ƙone motarsa highlander jeep da wasu dukiyoyinsa yayin harin.

Lamarin wanda ya faru ranar Alhamis da daddare, ya zo ne awanni 24 bayan arangama tsakanin matasa da sojoji a yankin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel