Sojoji sun ragargaji 'yan bindiga, sun ceto mutum 6 da aka yi garkuwa da su

Sojoji sun ragargaji 'yan bindiga, sun ceto mutum 6 da aka yi garkuwa da su

  • Sojoji sun yi nasarar ceto matafiya shida da aka yi garkuwa da su a Ekiti
  • Sunday Abutu, mai magana da yawun yan sandan jihar Ekiti ya tabbatar da lamarin
  • Wani da abin ya faru a idonsa ya ce wasu da suka sha da kyar ne suka kira sojojin

Ekiti - Sojoji sun yi nasarar ceto wasu mutane shida da yan bindiga suka yi garkuwa da su a jihar Ekiti kamar yadda ya zo a ruwayar The Cable.

A cewar NAN, an ceto mutanen ne yayin da sojojin suka fafata da yan bindigan a wurare biyu a Ayebode da Illasa a karamar hukumar Ikole ta jihar Ekiti.

Wasu ganau sun ce lamarin ya faru ne a ranar Alhamis hakan yasa matafiya suka kauracewa babban titin Ayedun-Ilasa-Ayebode na tsawon awonni.

Kara karanta wannan

Dakarun sojoji sun yi arangama da matasa a Imo, an ƙone gidaje da dama

Sojoji sun ceto mutane 6 da aka yi garkuwa da su bayan fafatawa da 'yan bindiga
Dakarun sojojin Najeriya. Hoto: Premium Times
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Bisa ruwayar Premium Times, tunda farko sojojin sun dakile yunkurin sace mutane har a wuri biyu hakan yasa aka yi nasarar ceto mutane shida.

Amma, daga bisani yan bindigan sun kuma sace wasu fasinjoji uku da suka taso daga Ayedun-Ekiti zuwa Illasa-Ekiti.

Wasu da abin ya faru a idonsu sun ce mutane ukun da yan bindigan suka sace suna tafiya ne kan hanyar Ayedun zuwa Ilasa a lokacin da maharan suka fara harbi.

Shaidan gani da idon ya ce:

"Wadanda suka tsere daga harin ne suka kira sojojin da ke kusa da wurin kuma suka amsa kirar cikin gaggawa."

Shaidan ya cigaba da cewa:

"Mutane biyun da ke cikin motar da suke tsere daga wurin sun samu karaya a kafafuwarsu, sannan akwai alamun harbin bindiga a motarsu.
"Sojojin sun yi nasarar fatattakar masu garkuwar zuwa cikin daji amma bana tunanin sun kama ko da daya ne cikinsu."

Kara karanta wannan

Bidiyon yadda ma'aurata suka sayo gida daga wani gari suka kawo shi garinsu

Kakakin yan sandan jihar Ekiti ya ce mutum hudu aka sace

Da ya ke tabbatar da afkuwar lamarin a ranar Juma'a, Sunday Abutu, kakakin yan sandan jihar ya ce hadin kan jamian tsaro ne ya sanya aka ceto mutum shida.

Ya ce:

"Bayanin da muka samu shine mutum hudu ne aka sace.
"Jami'an tsaro sun iso cikin gaggawa suka kuma ceto mutum shida.
"Mun fara bincike kuma za mu yi kokarin ganin an dawo da wadanda aka sace din cikin koshin lafiya."

Yunwa ya saka 'yan bindiga a gaba, sun nemi a basu dafaffen abinci a matsayin kudin fansa

A wani labarin, kun ji cewa Ƴan bindiga a ƙaramar hukumar Birnin Gwari a jihar Kaduna sun fara tambayar dafaffen abinci a matsayin kuɗin fansa, rahoton Daily Trust.

Ƴan bindigan sun janye kai hare-hare a garuruwa tun bayan da gwamnatin jihar ta soke cin kasuwannin mako-mako don daƙile rashin tsaro.

Kara karanta wannan

Bayan kimanin kwanaki 120, Dogo Giɗe ya sako ɗaliban Yauri 28 da malamansu biyu da ke hannunsa

Wani shugaban matasa a ɗaya daga cikin ƙauyukan Birnin Gwari, Babangida Yaro ya shaidawa Daily Trust cewa tun bayan hana cin kasuwanni ƴan bindiga da ke sace mutane a ƙauyukan Kutemashi da Kuyello dafaffen abinci suke tambaya duk lokacin da suka sace mutane.

Asali: Legit.ng

Online view pixel