Yunwa ya saka 'yan bindiga a gaba, sun nemi a basu dafaffen abinci a matsayin kudin fansa

Yunwa ya saka 'yan bindiga a gaba, sun nemi a basu dafaffen abinci a matsayin kudin fansa

  • Wasu masu garkuwa da mutane a Birnin Gwari a Kaduna sun fara tambayar dafaffen abinci
  • Babangida Yaro, shugaban matasa a Birnin Gwari ya tabbatar da cewa ƴan bindigan girki suke tambaya a matsayin kuɗin fansa
  • Hakan ya faru ne sakamakon hana cin kasuwannin mako-mako da gwamnatin jihar Kaduna ta yi don daƙile yan bindigan

Birnin Gwari, Kaduna - Ƴan bindiga a ƙaramar hukumar Birnin Gwari a jihar Kaduna sun fara tambayar dafaffen abinci a matsayin kuɗin fansa, rahoton Daily Trust.

Ƴan bindigan sun janye kai hare-hare a garuruwa tun bayan da gwamnatin jihar ta soke cin kasuwannin mako-mako don daƙile rashin tsaro.

Yunwa ya saka 'yan bindiga a gaba, sun nemi a basu dafaffen abinci a matsayin kudin fansa
Yunwa ya fitini 'yan bindigan Kaduna, sun fara tambayar girki a matsayin kudin fansa. Hoto: Daily Trust
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Mutum ɗaya ne ya sha barasa, Ɗaliban makarantar Qur'ani sun maida martani kan mummunan azabtarwa

Wani shugaban matasa a ɗaya daga cikin ƙauyukan Birnin Gwari, Babangida Yaro ya shaidawa Daily Trust cewa tun bayan hana cin kasuwanni ƴan bindiga da ke sace mutane a ƙauyukan Kutemashi da Kuyello dafaffen abinci suke tambaya duk lokacin da suka sace mutane.

A cewarsa, hana siyar da man fetur a gidajen mai da ke ƙauyuka ya taimaka wurin rage zirga-zirgan mutane.

Ya ce:

"An fara samun zaman lafiya a Dumari, Kuyello, Kutemashi, ƴan bindiga sun dena kai hari. A daji suke tsayawa suna kwace abinci galibi dafaffen abinci daga masu sayarwa."

Ya kara da cewa idan sun sace mutum uku, suna ƙyalle guda ɗaya ya tafi guda ya kawo musu abinci daga wurin ƴan uwansa tunda babu hanyar sadarwa.

Shugaban matasan ya kara da cewa har yanzu ba a samu cikakken tsaro ba a Dogon Dawa domin mutane suna tsoron zuwa gonakin su.

Babangida ya ƙara da cewa hana hawa babura wadanda ba na haya ba ya jefa mutanen gari da ƴan bindigan a cikin mawuyacin hali.

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari ne ɗan siyasan da yafi kowane farin jini da Nagarta a wannan zamanin, Osinbajo

Yadda wadanda aka yi garkuwa da su suka shafe kwanaki 53 sun cin ciyawa

A wani labarin, wasu daga cikin wadanda aka yi garkuwa da su a sassa daban-daban na jihar Zamfara sun koma cin ciyawa domin kada su mutu a yayin da wadanda suka sace su suka rasa abincin ba su.

Daya daga cikin wanda abin ya faru da su wacce ta ce sunanta Iklima Murtala, ta yi ikirarin cewa mutane 17 sun mutu saboda tsananin yunwa, ruwaiyar Daily Trust.

Kwamishinan 'yan sanda a jihar ta Zamfara, Ayuba Elkana, ya ce saboda matsin lambar da rashin abinci, 'yan bindigan sun tsinci kansu a mawuyacin hali.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164