Da duminsa: Bayan harin yan ta'adda, jirgin kasan Abuja/Kaduna zai koma aiki ranar Asabar

Da duminsa: Bayan harin yan ta'adda, jirgin kasan Abuja/Kaduna zai koma aiki ranar Asabar

  • Bayan kwana daya da dakatad da jirgin kasa, za'a cigaba da aiki ranar Asabar
  • Minista ya ce an kammala dukkan gyaran wuraren da aka lalata
  • Yan Najeriya sun tofa albarkatun bakinsu kan wannan lamari

Kaduna - Ministan Sufurin Najeriya, Rotimi Amaechi, ya bayyana cewa jirgin kasan Abuja-Kaduna zai cigaba da aiki daga gobe Asabar, 23 ga watan Oktoba 2021, rahoton DN.

A jawabin da yayi lokacin ziyarar ganin ido da ya kai inda yan ta'adda suka dasa nakiya ranar Juma'a, Amaechi yace gwamnati na aiki tukuru don damke yan bindigan da sukayi wannan aika-aika.

Ya bayyana cewa tuni an kammala gyara aka lalata kuma jirgin zai iya cigaba da aiki.

Yace:

"Idan na koma Abuja gobe, an hadu da shugabannin hukumar DSS da kuma shugaban Sojojin kasa. Sai mun nemo mutanen nan."

Kara karanta wannan

Jiragen NAF sun yi wa 'yan ISWAP luguden wuta yayin da suke cikin jiragen ruwa 11

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Da duminsa: Bayan harin yan ta'adda, jirgin kasan Abuja/Kaduna zai koma aiki ranar Asabar
Da duminsa: Bayan harin yan ta'adda, jirgin kasan Abuja/Kaduna zai koma aiki ranar Asabar Hoto: dailynigerian.com
Asali: UGC

Bincike: 'Yan ta'addan ISWAP da Ansaru ne suka sanya bam a layin dogon Abuja zuwa Kaduna

'Yan ta'addan kungiyar ta'addancci ta ISWAP tare da Ansaru ne suke da alhakin lalata layin dogon Abuja zuwa Kaduna, majiyoyi masu karfi na tsaro suka tabbatar wa da Daily Trust a ranar Alhamis.

Karaikainar jiragen kasa daga Abuja zuwa Kaduna ta gurgunta na wucin-gadi daga daren Laraba zuwa Alhamis bayan an gano cewa 'yan ta'adda sun sanya bam tare da tashin wani sashi na layin dogon.

Miyagun sun koma da sa'o'in farko na ranar Alhamis inda suka sake lalata wani sashi na layin dogon, lamarin da yasa hukumar jiragen kasa ta Najeriya ta dakatar da ayyukan ta.

Wani babban jami'in tsaro ya tabbatar wa da Daily Trust cewa, a cikin kwanakin da suka gabata, jami'an tsaro sun tare da halaka wasu 'yan ta'addan da suka yi yunkurin saka bam a gadoji da layikan dogo a Kaduna.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Yan bindiga sun sake kai hari ofishin yan sanda, sun saki fursunoni

"Wannan farmakin su na da hatimin ISWAP da Ansaru, 'yan bindiga sun so sace mutane tare da bukatar kudin fansa amma wannan ta'addanci ne a bayyane," yace.

“Sun so kashe mutanen da ke jirgin kasan. Amma muna godiya ga Ubangiji da ba su yi nasarar ba."

Asali: Legit.ng

Online view pixel