Bayan ƙwace motarsa da IPhone, Alƙali ya umarci ɗan 'Yahoo-Yahoo' ya yi sharar harabar kotu na watanni 6

Bayan ƙwace motarsa da IPhone, Alƙali ya umarci ɗan 'Yahoo-Yahoo' ya yi sharar harabar kotu na watanni 6

  • Babbar kotu da ke zama a Ibadan ta umarci wani dan damfarar yanar gizo, Adewale Tosin da sharar harabar kotun na watanni 6
  • Hakan ya biyo bayan amsa laifin sa da ya yi na damfarar wani baturen Amurka dala 2,400 bayan ya dinga yaudarar sa a matsayin mace
  • Alkalin ya yanke ma sa wannan hukuncin ne sannan ya nemi matashin ya biya baturen kudin sa, sannan gwamnati za ta kwace motar sa da wayarsa

Ibadan - Alkalin babbar kotu da ke zama a Ibadan ya yanke wa Adewale Tosin, dan damfarar yanar gizo hukuncin share harabar kotun na tsawon watanni 6 bisa ruwayar Premium Times.

Alkali Bayo Taiwo ya yanke wa Tosin wannan hukuncin ne bayan ya amsa laifin sa na damfarar wani bature dan Amurka.

Kara karanta wannan

Shugaban wurin aiki ya ba na ƙasa da shi da ke tashi cikin dare ya fara tattaki zuwa wurin aiki kyautar mota

Alƙali ya umarci ɗan 'Yahoo-Yahoo' ya yi sharar harabar kotu na watanni 6
Alƙali ya umarci ɗan 'Yahoo-Yahoo' ya yi sharar harabar kotu na watanni 6. Hoto: Daily Nigerian
Asali: UGC

Har ila yau, Daily Nigerian ma ta ruwaito yadda saurayin ya dinga yaudarar baturen, Zielone Nyson a matsayin mace mai suna Lylian Zamarippa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sai da Taiwo ya warwari Nyson kudi dala 2,400. Don haka alkalin ya umarce shi da asubancin share kotun, inda ya ce karfe 8am ta dinga yi ma sa a harabar kotun.

Kada ya kuskura ya yi fashi ko kuma latti

Alkalin ya kara da cewa dole ne rana ta dinga ma sa ya na wa al’umma hidima kuma zai kasance ne a kowacce ranar aiki ta mako.

Alkalin ya ce:

“Mai laifin zai yi shekaru 2 a gidan kaso idan har ya ki zuwa shara kotun ko kuma ya yi latti ko sau daya, ko da kuwa ranar sa ce ta karshe a aikin.
“Sannan wajibi ne ya mayarwa da wanda ya damfara dala 2,400 sannan gwamnatin tarayya za ta kwace motarsa kirar SUV, na’ura mai kwakwalwa da wayarsa kirar iPhone.”

Kara karanta wannan

Bayan rayuwa cikin daji yana cin ciyawa, yanzu wankan sutturu na alfarma ya ke yi, ana girmama shi a gari

Lauyan mai kara, Festus Ojo ya sanar da kotu yadda mai laifin ya aikata damfarar tsakanin watan Fabrairun 2020 da Janairun 2021.

Lauyan wanda ake kara, M. A. Rufai ya roki kotu ta ci tarar mai laifin a maimakon dibar ma sa shekarun da ta yi a gidan gyaran hali.

An sha mamaki bayan gano cewa gardin namiji aka tura gidan yari na mata ba tare da an gane a kotu ba

Wani lamari mai ban mamaki ya auku a gidan gyaran halin mata da ke Shurugwu a makon da ya gabata, inda aka gano wata fursuna ba mace bace, katon namiji ne kamar yadda LIB ta ruwaito.

Praise Mpofu mai shekaru 22 ya na sanye da suturar mata ne a lokacin da aka kama shi inda ya bayyana kamar karuwa don ya yaudari maza ya yi musu sata.

An kama Mpofu ne bayan ya yi wa wani mutum da ke yankin Gweru sata. An samu rahoto akan yadda mutumin ya caskewa Mpofu kudi don su kwana tare da shi a tunanin sa mace ne, daga nan Mpofu ya yashe shi ya tsere.

Kara karanta wannan

Wakilin Birtaniya ya dira kotu domin shari'ar shugaban 'yan awaren IPOB

Asali: Legit.ng

Online view pixel