Bayan rayuwa cikin daji yana cin ciyawa, yanzu wankan sutturu na alfarma ya ke yi, ana girmama shi a gari

Bayan rayuwa cikin daji yana cin ciyawa, yanzu wankan sutturu na alfarma ya ke yi, ana girmama shi a gari

  • Wani matashi, Nsanzimana Elie wanda ya yi rayuwa cikin daji mutane su na kushe halittar sa yanzu ya daukaka
  • Alamu sun nuna cewa Ubangiji ya amshi addu’ar mahaifiyar sa bayan mutuwar yaran ta 5 saura shi kadai
  • Bayan bayyanar hotunan sa, mutanen kirki su ka dinga taimaka ma sa, yanzu haka ya daukaka a kauyen su

Rwanda - Wani matashi, Nsanzimana Elie ya kasance a baya ya na zama cikin daji saboda yanayin suffar sa, sannan mutanen kauyen sa har tonon sa su ke yi.

Akwai wadanda su ke kiran sa da biri, ashe daukaka ta na nan biye da shi, kamar yadda Legit.ng ta ruwaito.

Mahaifiyar Elie ta ce Ubangiji ya amshi addu’ar ta na ba ta shi da ya yi bayan yaran ta 5 duk sun rasu, kuma ba ta kunyar nuna shi.

Kara karanta wannan

Ba zama: Wani mutum ya yi garkuwa da dan sufeton 'yan sanda

Bayan rayuwa cikin daji yana cin ciyawa, yanzu wankan sutturu na alfarma ya ke yi, ana girmama shi a gari
Nsanzimana Elie, watanni 9 da suka shude lokaci yana rayuwa a daji. Hoto: Afrimax TV
Asali: Instagram

A watan Fabrairu ne labarin sa ya yawaita a yanar gizo wanda hakan ya janyo mutane da dama su ka taimaka ma sa bisa ruwayar Legit.ng.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yanzu kusan watanni 9 kenan, Elie mai shekaru 21 daga kudancin Rwanda ya samu daukaka har gidan talabijin na Afrimax da ke kasar su sun nuna shi.

Ya yi rayuwa a daji tamkar gwaggon biri saboda yanayin surar da Ubangiji ya yi masa wanda mutane su ka dinga kashewa.

Bayan samun kudade masu kauri daga jama’a daban-daban ashe ta nan daukaka take biye da shi.

Ah haifi Elie a shekarar 1999 ne bayan mahaifiyar sa ta rasa yara har 5 sannan ta same shi.

Bayan rayuwa cikin daji yana cin ciyawa, yanzu wankan sutturu na alfarma ya ke yi, ana girmama shi a gari
Nsanzimana Elie bayan mutane masu fatan alheri sun tallafa masa. Hoto: Afrimax TV
Asali: Instagram

Mahaifiyarsa ta cire rai da haihuwa sannan ta same shi

A wata tattaunawa da aka yi da mahaifiyar sa, ta ce har ta cire rai da samun haihuwa sai ga shi ta haifi Elie duk da ba ya da cikakkiyar lafiya.

Kara karanta wannan

Buhari ya fusata da halin 'yan bindiga: Yanzu kam kwanakinku sun kusa karewa

Ta ce:

“Elie da na ne na 6. Duk yayyin sa 5 sun mutu. Bayan mutuwar su mun shiga damuwa. Mun roki Ubangiji ya bamu haihuwa shi ne ya azurta mu da Elie.
"Yanzu haka ina mutukar farincikin wannan kyautar da Ubangiji ya yi mana kuma ina matukar son sa.”

Ta ce tun bayan haihuwar sa ta san halittar sa ta daban ce saboda kan sa karami ne sosai sannan fuskar sa daban ce.

Daga baya a ka gano cewa ba ya iya magana sannan ya na da matsalar fahimtar karatu.

Da farko ba ya ko zuwa makaranta saboda ba ya gane komai kuma ba ya iya magana da kowa.

Likitoci sun bayyana wa mahaifiyar sa cewa yaron ba zai iya koyon karatu ba sai dai abinda ba za a rasa ba.

Ya fi son rayuwa cikin daji

Yayin da yake tasowa, ya fi son rayuwa cikin daji ya na cin ganye. A cewar ta kusan kullum sai ta koro shi daga daji.

Kara karanta wannan

Na yi gyaran kwata ana biya na N20: Ɗan kwallo mafi tsada a Afirka kuma tauraron Super Eagles, Victor Osimhen

Ta kara da bayyana yadda yake guduwa idan ya ga mutane saboda tsoron su yake yi, wani lokacin har daure shi da igiya take yi.

A cewar ta:

“Idan na ji wani ya na zagin sa ko zaluntar sa ko kuma kiran sa da biri, rai na ya na matukar baci. Na san ba laifin sa ba ne kuma ba ya cutar da kowa."

Bayan watanni kadan da labarin sa ya yadu a yanar gizo, mutane su ka gina ma sa sabon gida kuma su ka sa ma sa kayan alatu a ciki.

Yanzu ya zama dan gayu kuma tsukewar sa ya ke yi cikin sutturu irin na zamani. Har son daukar hotuna ake yi tare da shi.

Kuma a hankali ya na koyon rayuwa cikin mutane maimakon zama a cikin daji.

Asali: Legit.ng

Online view pixel