Da dumi-dumi: FG ta gano masu daukar nauyin Igboho, ta bayyana yadda aka tura masa miliyoyin naira a asusunsa

Da dumi-dumi: FG ta gano masu daukar nauyin Igboho, ta bayyana yadda aka tura masa miliyoyin naira a asusunsa

  • Gwamnatin tarayya ta ce ta bankado masu daukar nauyin dan fafutukar nan na kasar yarbawa, Sunday Adeyemo, wanda aka fi sani da Sunday Igboho
  • FG ta kuma gano yadda masu daukar nauyin nasa suka dunga tura masa miliyoyin naira ta asusu 43 a bankuna tara
  • Ministan shari’a, Abubakar Malami, ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai a Abuja a ranar Juma’a, 22 ga watan Oktoba

Abuja - Gwamnatin tarayya ta gano masu daukar nauyin dan fafutuka na kasar yarbawa, Sunday Adeyemo, wanda aka fi sani da Sunday Igboho.

Atoni Janar na tarayya kuma ministan shari’a, Abubakar Malami, ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai a Abuja a ranar Juma’a, 22 ga watan Oktoba, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Da dumi-dumi: FG ta gano masu daukar nauyin Igboho, ta bayyana yadda aka tura masa miliyoyin naira a asusunsa
Da dumi-dumi: FG ta gano masu daukar nauyin Igboho, ta bayyana yadda aka tura masa miliyoyin naira a asusunsa Hoto: #sundayIgboho
Source: Facebook

A cewar Malami, wani kwamiti da gwamnatin tarayya ta kafa ta bankado yadda Igboho ya samu kudade daga asusun bankuna 43, a fadin bankuna tara.

Read also

PDP na bukatar mutane masu mutunci domin lashe zaben shugaban kasa a 2023 - Fintiri

Ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Gwamnatin tarayya ta karbi rahoto kon masu daukar nauyin Sunday Adeyemo wanda aka fi sani da Sunday Igboho. Rahoton ya bayyana cewa Sunday Igboho shine daraktan kamfanin Adesun International Concept Limited wanda aka yi rijista a ranar 23 ga watan Afrilu, 2010.
“Har ila yau kamfanin Adesun International Concept Limited na da Oladele Oyetunji da Aderopo Adeyemo a matsayin daraktoci. An gano Sunday Igboho yana da nasaba da asusun banki 43 a bankuna 9.
“An gano cewa babban mai daukar nauyin dan awaren ya kasance dan majalisa a majalisar dokokin tarayya. Igboho ya karbi jimlar kudi N127, 145,000.00 daga hannun masu daukar nauyinsa a tsakanin 22 ga watan Oktoba 2013 da 28 ga watan Satumban 2020 ta asusun kamfanin Adesun International Concept Ltd.
“Jimlar kudi N273,198,200.00 ne suka fita daga asusun Igboho tsakanin 15 ga watan Maris 2013 da 11 ga watan Maris 2021.

Read also

Farashin Shayi 'Empty' ya tashi a jihar Kano, Kakaakin Masu Shayi

“Bincike ya nuna cewa kamfanin Adesun International Concept Ltd (mallakin Igboho) ya tura N12, 750,000 zuwa kamfanin Abbal Bako & Sons.
“Ana iya tuna cewa ana zargin Abbal Bako & Sons da mai tallata shi Abdullahi Umar Usman a binciken hadin gwiwa na masu daukar nauyin ta’addanci da ke gudana. Abdullahi Umar Usman yana da alakar hada-hadar kudi da SURAJO ABUBAKAR MUHAMMAD (wanda aka yanke wa hukuncin daurin rai da rai a daular larabawa kan daukar nauyin ta’addanci wato Boko Haram).
“Wannan rahoton ya nuna alakar dake tsakanin fafutukar dan awaren, masu daukar nauyin ta’addanci da kawo cikas ga zaman lafiya a kasar.
“Rahoton ya gano alaka ta hada-hadar kudi tsakanin kamfanin Adesun International Concept Ltd (mallakin Igboho) da wasu kamfanonin gine-gine da kasuwanci da sauransu.”

An garzaya da Sunday Igboho asibiti daga Kurkuku, ya kamu da cutar Koda

A wani labarin, mun kawo cewa an garzaya da mai rajin kafa kasar Oduduwa, Sunday Adeyemo wanda akafi sani da Sunday Igboho asibiti bayan kamuwa da cutar koda da yayi a Kurkukun Kotonou.

Read also

Sai mun hada kai ne za mu iya cin galaba a kan miyagu – APC kan harin jirgin kasa

Daya daga cikin Lauyoyinsa, Yomi Aliyu, ya bayyana hakan ne a hirar da yayi da BBC Yoruba.

A cewar, Sunday Igboho na fama da matsanancin rashin lafiya kuma an garzaya da shi asibiti.

Source: Legit.ng

Online view pixel