An garzaya da Sunday Igboho asibiti daga Kurkuku, ya kamu da cutar Koda
- Sunday Igboho ya kamu da rashin lafiya cikin gidan yari a kasar Benin
- Gwamnatin Kotono ta garkameshi cikin Kurkuku kan laifin kokarin shiga kasar da takardun bogi
- Janar Buratai (mai ritaya) ne Jakadan Najeriya zuwa kasar Benin
An garzaya da mai rajin kafa kasar Oduduwa, Sunday Adeyemo wanda akafi sani da Sunday Igboho asibiti bayan kamuwa da cutar koda da yayi a Kurkukun Kotonou.
Daya daga cikin Lauyoyinsa, Yomi Aliyu, ya bayyana hakan ne a hirar da yayi da BBC Yoruba.
A cewar, Sunday Igboho na fama da matsanancin rashin lafiya kuma an garzaya da shi asibiti.
Yomi Aliyu yace:
"Igboho bai kamu da cutar nan kafin tsareshi a Kotono ba. Abin yayi muni da ya kai sai da aka garzaya da shi asibiti."
"Ban sani ko yanzu sun mayar da shi Kurkuku daga asibiti ba, amma yana fama da matsanancin rashin lafiya kuma da alamun abin ya shafi kodarsa da huhunsa."
Wasu daga cikin kungiyar Ilana Omo Oodua sun tabbatar rashin lafiyar Igboho.
Wani ya bayyanawa Punch cewa:
"Lallai yana fama da rashin lafiya kuma da alamun ya shafi kodarsa. Bamu tabbatar ba tukun don sai an sake gwaji. Muna kokarin ganin cewa yana samun kula mai kyau."
Dan majalisar tarayya ke daukar nauyin Sunday Igboho da Nnamdi Kanu, Buhari ya yi ikirari
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi ikirarin cewa wani dan majalisar tarayya ne ke da alhakin daukar nauyin masu kira-kirayen neman ballewar kasar nan.
Shugaban kasar ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi ga kasar a matsayin wani bangare na bikin ranar 'yancin kai.
Ya bayyana cewa an gano hakan ne yayin da ake gudanar da bincike bayan kamun Nnamdi Kanu, shugaban masu fafutukar neman kasar Biyafara da kuma Sunday Igboho, shugaban masu fafutukar kasar Yarbawa.
“Kamen da aka yi kwanan nan na Nnamdi Kanu da Sunday Adeyemo, da kuma binciken da ake gudanarwa ya nuna wasu manyan masu kudi ne a bayan wadannan mutane," yace.
Asali: Legit.ng