Da duminsa: Nnamdi Kanu ya bayyana a gaban kotu, an hana 'yan jarida shiga

Da duminsa: Nnamdi Kanu ya bayyana a gaban kotu, an hana 'yan jarida shiga

  • Hukumar DSS ta gabatar da shugaban IPOB, Nnamdi Kanu, a gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja
  • Shugaban lauyoyin Kanu, Barista Ifeanyi Ejiofor ne ya tabbatar da hakan tare da bayyana hotunansu tare a dakin kotun
  • Har a lokacin rubuta wannan rahoton, jami'an tsaro sun haramtawa 'yan jarida shiga farfajiyar zauren kotun

FCT, Abuja - Shugaban 'yan awaren IPOB, Nnamdi Kanu, ya gurfana a gaban kotu bayan wasu jami'an hukumar tsaro ta farin kaya sun kawo shi domin fuskantar shari'a.

An shigar da shi zauren kotun ne yayin da aka tsananta tsaro tare da hana manema labarai daukar bidiyo ko hotunansa, jaridar Punch ta wallafa.

Barista Ifeanyi Ejiofor, shugaban lauyoyi masu kare Kanu, ya tabbatar da hakan ga manema labarai. Ya ce wanda ya ke karewa ya na cikin zauren kotun kuma ya bayyana hotunsu tare.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Nnamdi Kanu ya musanta zargin da ake masa a gaban kotu

Da duminsa: Nnamdi Kanu ya bayyana a gaban kotu, an hana 'yan jarida shiga
Da duminsa: Nnamdi Kanu ya bayyana a gaban kotu, an hana 'yan jarida shiga. Hoto daga thenationolineng.net
Asali: UGC

An kawo Nnamdi Kanu kotun ne yayin da aka tsananta tsaro tare da tawagar jami'an tsaro wurin karfe takwas da minti uku.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A lokacin rubuta wannan rahoton, babu dan jarida da aka bari ya shiga farfajiyar zauren kotun, Channels TV ta ruwaito.

Jami'an DSS tun farko sun saka shinge a hanyar shiga babbar kotun tarayyar, inda za a saurari shari'ar kuma suka hana manema labarai daga shiga, lamarin da ya fusata jama'a masu yawa.

Wannan na zuwa ne bayan kwanaki uku da gwamnatin tarayya ta shigar da gyararrun kararraki 7 kan Kanu wadanda suka hada da cin amanar kasa da kuma ta'addanci.

Alkalin da za ta saurari kara, Mai shari'a Binta Nyako, ta saka yau ranar 21 ga watan Oktoba sakamakon rashin ganin Kanu a gaban kotu a ranar Litinin.

Ta jaddada cewa, ba za a cigaba da shari'ar ba har sai Kanu ya na nan.

Kara karanta wannan

An ba mata masu ciki, masu shayarwa damar NYSC a garuruwan mazajensu

Wakilin Birtaniya ya dira kotu domin shari'ar shugaban 'yan awaren IPOB

A wani labari na daban, wakilin Birtaniya a Najeriya ya isa babbar kotun tarayya da ke Abuja domin sauraron shari'ar shugaban 'yan awaren IPOB, Nnamdi Kanu.

TheCable ta ruwaito cewa, wakilin Ingilan ya isa farfajiyar kotun a wata mota fara kirar Toyota Highlander wurin karfe takwas da minti uku na safiyar ranar Alhamis.

Kanu wanda ke da shaidar zama dan kasar Birtaniya, ya shiga hannun hukuma a Najeriya ne a watan Yuni kuma an dawo da shi gida Najeriya domin a gurfanar da shi kan zargin cin amanar kasa da ake masa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel