Rahoto: 'Yan bindiga sun sace sama da mutane 830 a jihar Kaduna cikin watanni 3

Rahoto: 'Yan bindiga sun sace sama da mutane 830 a jihar Kaduna cikin watanni 3

  • Kwamishinan tsaro da harkokin tsaron cikin gida ya bayyana rahoton tsaro na watanni uku
  • Ya bayyana adadin mutanen da aka sace a fadin jihar, tare da yadda aka hallaka 'yan bindiga a Kaduna
  • Ya kuma bayyana adadin sace-sace da kai hare-hare kan makarantu a bangarori daban-daban na jihar

Kaduna - Daily Trust ta ruwaito cewa, kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Kaduna, Samuel Aruwan, ya ce an yi garkuwa da mutane 830 a jihar daga watan Yuli zuwa Satumba 2021.

Ya bayyana hakan yayin gabatar da rahoton tsaro na kwata na 3 ga gwamnan jihar, Nasir El’rufai, ranar Laraba 20 ga watan Oktoba.

A rahoton Daily Sun, Aruwan ya kuma ce sojojin sun kashe jimillar 'yan ta'adda 69 a lokacin da suke kai hare-hare a sassa daban-daban na jihar a cikin wannan lokaci da ya ambata.

Kara karanta wannan

Buhari ya fusata da halin 'yan bindiga: Yanzu kam kwanakinku sun kusa karewa

'Yan bindiga sun sace sama da mutane 800 a jihar Kaduna cikin watanni 3
Kwamishinan tsaro, Samuel Aruwan | Hoto: Samuel Aruwan
Asali: UGC

Ya yi bayanin cewa an kashe 'yan ta'adda da yawa yayin hare-hare ta sama kan wuraren da aka gano suna fakewa sannan an lalata sansanonin 'yan ta'adda da yawa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kwamishinan ya ce daga cikin wadanda aka yi garkuwa da su a gundumar sanatan Kaduna ta tsakiya sun kai 732 a wurare kamar kananan hukumomin Birnin Gwari, Giwa, Igabi, Chikun da Kajuru.

Ya kuma ce an sace dabbobi 1,018 a jihar a cikin kwata na uku na shekarar tare da sace mutane 780 daga gundumar sanatan Kaduna ta tsakiya.

Aruwa ya kuma ce mutanen da suka jikkata a fadin jihar dalilin barnar 'yan bindiga, hare-haren ta'addanci, ramuwar gayya da kuma rikice-rikicen al'ummomi sun kai 210.

Ya koka da cewa an samu rahotanni 77 da suka shafi lalata amfanin gona a fadin jihar musamman a kananan hukumomin Birnin Gwari, Igabi, Giwa, Chikun, Kachia, Kaura, Kauru da Zongon Kataf.

Kara karanta wannan

An kashe manoma uku a wani sabon hari da aka kai kan kauyen Filato

Gwamna El-Rufai zai fara hana ma'aikatan da basu yi rigakafin Korona ba shiga ofis

Gwamnatin jihar Kaduna ta yanke shawarin daukar mataki kan ma'aikatan gwamnatin jihar da ba su yi allurar rigakafin Korona ba.

Wata sanarwa da gwamna El-Rufai ya fitar a shafinsa na Facebook dauke da sa hannun Muyiwa Adekeye, mai ba gwamnan shawara kan harkokin yada labarai ta bayyana dalilin daukar matakin.

Gwamnatin ta ce, daga ranar 31 ga watan Oktoba za a hana ma'aikatan gwamnatin da basu yi allurar rigakafi ba shiga ofisoshin gwamnati.

Asali: Legit.ng

Online view pixel