Gwamnan jihar Kwara na zargin Ministan Buhari Lai Mohammed ya yi rub-da-ciki da N100million

Gwamnan jihar Kwara na zargin Ministan Buhari Lai Mohammed ya yi rub-da-ciki da N100million

  • Gwamnan Kwara ya ce Ministan Labarai yayi babakeren miliyoyin kudade
  • A cewarsa, Lai Mohammed ba aminin mutum bane
  • Wannan ya biyo bayan rikicin siyasar dake gudana tsakanin gwamnan da Ministan

Gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman Abdul Razzzak, ya tuhumci Ministan Labarai da al'adu Alh Lai Mohammed da rub-da-ciki da miliyoyin nairori na yakin neman zabe.

Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin hira da jaridar ThisDay ranar Lahadi.

A cewarsa, gwamnan jihar Kaduna da wani attajiri daga kasar Igbo sun tura masa kyautan kudi amma Ministan Buhari ya rike kudaden.

Gwamnan yace:

"Shugaban ma'aikatan gwamnan jihar Kaduna ya kira yace in turo lambar akawunt na banki su turo min kudi. Da nace a bada, sai aka ce Lai (Mohammed) ya basu lambar akawunt nasa kuma an tura masa.

Read also

Abun bakin ciki: Yadda ‘da ya kashe mahaifinsa a kan gona a jihar Gombe

"Toh har yau shiru kake ji, bai fada mana ya karbi kudi ba."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ministan Buhari Lai Mohammed ya yi rub-da-ciki da N100million, Gwamnan jihar Kwara
Ministan Buhari Lai Mohammed ya yi rub-da-ciki da N100million, Gwamnan jihar Kwara

Irin wannan ya sake faruwa bayan na El-Rufa'i

Gwamnan ya kara da cewa bayan haka, wani attajirin dan kasuwa dan kabilar Igbo ya kira don bada nasa gudunmuwar.

A cewarsa:

"Akwai wani attajiri daga yankin Igbo. Manajan bankinsa yazo yace min maigidansa na son min magana. Na yi magana da shi kuma yace min zai turo wasu kudade, na ce masa na gode."
"Bayan zaben, ya kira ni don tayani murna, amma da yaji kawai nagode nike cewa, sai ya tambayeni shin ban samu sakonsa daga wajen Lai bane, sai na tambayesa wani kudi? yace N100m"

Gwamnan yace Lai Mohammed yayi rub-da-ciki da kudaden gaba daya bai basa ba.

Ko aben gundumarsa ba ai iya ci ba, Gwamnan jihar Kwara, Abdulrahman Abdulrazaq, ya soki ministan yaɗa labarai, Alhaji Lai Muhammed

Read also

Sakin Nnamdi Kanu zai kawo ƙarshen rashin tsaro a kudu maso gabas, Sanata Ubah

Gwamnan jihar Kwara, Abdulrahman Abdulrazaq, yace ministan yaɗa labarai, Lai Muhammed, ba zai iya komai ba a siyasance.

Gwamnan ya bayyana cewa ministan ya fi kwari a wajen ɓaɓatu da surutu a kafafen sada zumunta da kuma na watsa labarai.

The Cable ta rahoto Abdulrazaq, yace tsaginsa na jam'iyyar APC shike da yan majalisun dokokin jihar baki ɗaya, banda mutum ɗaya wanda yake tare da ministan.

Source: Legit

Online view pixel