Abun bakin ciki: Yadda ‘da ya kashe mahaifinsa a kan gona a jihar Gombe

Abun bakin ciki: Yadda ‘da ya kashe mahaifinsa a kan gona a jihar Gombe

  • Al'umman kauyen Zange da ke karamar hukumar Dukku ta jihar Gombe sun wayi gari da wani mummunan lamari a ranar Asabar
  • Hakan ya kasance ne bayan wani mutumi mai suna Haruna Buba, dan shekaru 32, ya kashe mahaifinsa a kan gona
  • Haruna dai ya sari mahaifin nasa da adda a kai da baya a lokacin da yayi kokarin yin sulhu tsakaninsa da wani yayansa wanda yayi zargin cewa an bai wa babban gona

Jihar Gombe - Wani mutumi mai shekaru 32 a duniya ya kashe mahaifinsa a ranar Asabar a kauyen Zange da ke karamar hukumar Dukku ta jihar Gombe a kan gona.

A cewar wata majiya, yaron mai suna Haruna Buba, ya aikata kisan ne biyo bayan wani sabani da yayi da yayansa, yayin da yake zargin mahaifinsu da bai wa yayan nasa babban gona.

Kara karanta wannan

An kashe manoma uku a wani sabon hari da aka kai kan kauyen Filato

Abun bakin ciki: Yadda ‘da ya kashe mahaifinsa a kan gona a jihar Gombe
Abun bakin ciki: Yadda ‘da ya kashe mahaifinsa a kan gona a jihar Gombe Hoto: Premium Times
Asali: UGC

An tattaro cewa mahaifin nasa, Habu Kuppe ya zo ne domin yin sulhu a tsakanin ‘yan uwan biyu lokacin da Haruna ya yanke shi a kai da baya da adda, inda a nan take ya fadi ya mutu.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa bayan ya kashe mahaifin nasa, sai Haruna ya tafi wajen kallo a kauyen, daga nan ne ‘yan sanda suka kama shi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Rahoton ya kuma nuna cewa da aka tuntubi kakakin ‘yan sandan jihar, Mallum Buba, ya tabbatar da lamarin, inda yace za a mika mai laifin zuwa kotu bayan bincike.

Babbar Magana: Wani dan Saurayi ya hallaka dan okada kan N500 na siyan Data a wayar salula

A wani labarin, jami'an yan sanda sun damƙe wani ɗan saurayi, Samson Odunayo, tare da abokan aikinsa biyu, bisa zargin kashe wani ɗan okada da sace mashin ɗinsa a jihar Ogun.

Kara karanta wannan

Tsoho mai shekaru 60 ya kashe ɗansa mai shekaru 32 saboda saɓani da ya shiga tsakaninsu

Punch ta rahoto cewa Odunayo, ɗan shekara 18, ya amince da laifin da ake zarginsa, amma yace ya yi haka ne saboda yana bukatar N500 na siyan Data.

Odunayo, ya shiga hannun yan sanda ne tare da sauran abokan aikata ta'asarsa, Sodiq Awokoya da Jimoh Rilwan a yankin Ogere ranar Jumu'a.

Asali: Legit.ng

Online view pixel