Gwamnan Bauchi ya tona asirin wadanda ke hada kai da 'yan ta'adda a jiharsa

Gwamnan Bauchi ya tona asirin wadanda ke hada kai da 'yan ta'adda a jiharsa

  • Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi ya zargi sarakunan gargajiya da taimakawa 'yan ta'adda a jiharsa
  • A cewar gwamnan, bata-garin su kan hada kai da jami'an tsaro marasa kishin kasa wurin aikata barna
  • Gwamnan ya yi kira ga kwamishinoninsa da su zage damtse wurin tabbatar da cewa tsaro ya tabbata a jihar

Bauchi -Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed a ranar Litinin, ya zargi 'yan ta'adda da hada kai da wasu sarakunan gargajiya tare da wasu bata-gari cikin jami'an tsaro wurin tada zaune tsaye a wasu yankunan jihar.

Daily Trust ta wallafa cewa, Mohammed ya sanar da hakan ne yayin taron majalisar zartarwa ta jihar Bauchi, inda ya jajanta wannan lamarin tare da tsanantawa wurin shawo kan matsalar tsaron jihar.

Gwamnan Bauchi ya tona asirin wadanda ke hada kai da 'yan ta'adda a jiharsa
Gwamnan Bauchi ya tona asirin wadanda ke hada kai da 'yan ta'adda a jiharsa. Hoto daga dailytrust.com
Source: UGC

Daily Trust ta wallafa cewa, a don haka ya yi kira ga kwamishinoninsa da sauran masu ayyukan taimako da su yi aiki tare da shugabannin kananan hukumomin jihar wurin inganta tsaro.

Read also

An kashe manoma uku a wani sabon hari da aka kai kan kauyen Filato

Ya ce duk da Bauchi ta na daga cikin jihohi masu zaman lafiya a arewa maso gabas, "ba mu bacci domin ganin mun tabbatar da kwanciyar hankali da yakar 'yan ta'adda."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Ku ne wakilai na; ya zama dole mu sauya tsarin rayuwarmu. Wadannan mutanen suna zuwa kuma suna hada kai da sarakunan gargajiyanmu tare da bata-gari a cikin jami'an tsaro, amma muna yin abinda ya dace," Mohammed ya sanar da kwamishinoni.
"Da yawa daga cikin kananan hukumomin jihar nan lamarin ya shafe su. Sun hada da Alkaleri, Toro, Ningi da Ganjuwa.
“Ya zama dole mu yi aiki tukuru saboda komai a duniyar nan ya dogara ne da rayuwa da kuma kadarori. Idan ka mutu, komai naka ya kare. Ganin cewa ana alakanta jihar nan da zama jiha ma fi zaman lafiya a arewacin Najeriya shi ke ba mu kalubale," yace.

Read also

Zamfara: A kalla rayuka 12 sun salwanta, 'yan bindiga sun kone motar 'yan sanda

A wani bangare kuwa, gwamnatin jiha ta kwace dukkan filayen da ta bada domin yin wuraren shakatawa da bude ido a jihar saboda al'amuran 'yan ta'adda a wuraren.

Kano: 'Yan sanda sun yi ram da matasa 3 da ke barazanar sace magidanci idan bai biya N2m ba

A wani labari na daban, jami'an rundunar 'yan sandan jihar Kano sun cafke wasu mutum 3 da ake zargi da garkuwa da mutane a kwatas din Sharada ta jihar.

Kakakin rundunar, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, wanda ya bayyana hakan a ranar Juma'a, ya ce an cafke wadanda ake zargin bayan an samu rahoton cewa suna barazanar sace wani mutum.

Mazaunin yankin ya tabbatar da suna kiransa a waya tare da bukatar kudi har naira miliyan biyu ko kuma su sace shi ko wani daga cikin iyalansa.

Source: Legit.ng

Online view pixel