Kano: 'Yan sanda sun yi ram da matasa 3 da ke barazanar sace magidanci idan bai biya N2m ba

Kano: 'Yan sanda sun yi ram da matasa 3 da ke barazanar sace magidanci idan bai biya N2m ba

  • Rundunar 'yan sandan jihar Kano ta tabbatar da cafke wasu matasa 3 da ke barazanar sace magidanci ko iyalansa
  • Magidancin mazaunin Kwanar Ganduje ya kai korafin wasu za su sace shi idan har bai ba su miliyan 2 ba
  • A baya ya taba tura musu miliyan 1 lokacin da suka yi masa irin barazanar, sannan suka kyale shi ya shaki iskar 'yanci

Kano - Jami'an rundunar 'yan sandan jihar Kano sun cafke wasu mutum 3 da ake zargi da garkuwa da mutane a kwatas din Sharada ta jihar.

Kakakin rundunar, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, wanda ya bayyana hakan a ranar Juma'a, ya ce an cafke wadanda ake zargin bayan an samu rahoton cewa suna barazanar sace wani mutum.

Mazaunin yankin ya tabbatar da suna kiransa a waya tare da bukatar kudi har naira miliyan biyu ko kuma su sace shi ko wani daga cikin iyalansa.

Kara karanta wannan

Zamfara: A kalla rayuka 12 sun salwanta, 'yan bindiga sun kone motar 'yan sanda

Kano: 'Yan sanda sun yi ram da matasa 3 da ke barazanar sace magidanci idan bai biya N2m ba
Kano: 'Yan sanda sun yi ram da matasa 3 da ke barazanar sace magidanci idan bai biya N2m ba. Hoto daga lindaikejisblog.com
Asali: UGC

Kiyawa ya ce mai korafin tun farko ya bai wa wadanda ake zargin naira miliyan daya bayan ikirarinsu, LIB ta ruwaito.

"A ranar 23 ga watan Satumba, mun samu rahoto daga wani mazaunin Kwanar Ganduje da ke Sharada a Kano cewa ana barazanar sace sa idan bai bada miliyan biyu ba, ko kuma wani daga cikin iyalansa," Kiyawa yace.
"Ya ce a cikin watan Augusta, an tuntube shi da wannan lambar wayar kuma an yi barazanar sacesa inda ya bada miliyan daya.
"Bayan samun korafin, kwamishinan 'yan sandan jihar Kano, CP Sama’ila Shu'aibu Dikko, ya bada umarni ga rundunar karkashin SP Shehu Dahiru da su bincika tare da cafko wadanda ke da hannu a ciki.
"Bayan bincike na musamman, an cafko Salihu Usman mai shekaru 24 daga Anguwan Rogo a jihar Filato, Mubarak Aliyu mai shekaru 18 daga yankin Duwala a jihar Filato da kuma Sahibul Husna Auwal mai shekaru 17 daga Kwanar Ganduje a kwatas din Sharada, Kano".

Kara karanta wannan

An biya dan Najeriya diyyar N17m bayan abokin aikinsa ya kira shi da goggon biri a Ireland

Binciken farko ya nuna cewa wadanda ake zargin sun amsa laifinsu kuma sun tura sakonni domin karbar miliyan biyu. Sun kuma tabbatar a baya sun karba miliyan daya daga gare shi.

Za a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu bayan kammala bincike.

Kaduna: 'Yan bindiga sun sako 3 daga cikin daliban makarantar horar da limaman coci da suka sata

A wani labari na daban, uku daga cikin daliban makarantar horar da limaman coci da aka sace na Christ the King Major Seminary a karamar hukumar Jema'a ta jihar Kaduna sun samu 'yancinsu.

Kamar yadda Daily Trust ta ruiwaito, shugaban makarantar, Rabaren Fada Emmanuel Uchechukwu Okolo, ya tabbatar da sakin su da aka yi a daren Laraba.

Ya ce cocin za ta cigaba da addu'a tare da fatan a sako sauran daliban da ke hannun masu garkuwa da mutanen.

Asali: Legit.ng

Online view pixel