Kaduna: Jami'an tsaro sun kashe 'yan bindiga da dama, sun banka wa sansaninsu wuta

Kaduna: Jami'an tsaro sun kashe 'yan bindiga da dama, sun banka wa sansaninsu wuta

  • Jami’an tsaro sun harbe ‘yan bindiga 10 a Kwanan Bataru, wajen Fatika, karamar hukumar Giwa a jihar Kaduna
  • Har ila yau sun banka wa maboyar ‘yan bindigan wuta inda su na kone ta kurmus
  • Akwai ‘yan bindiga da yawa wadanda su ka raunana saboda musayar wuta da jami’an tsaro

Kaduna - Jami’an tsaro sun harbe ‘yan bindiga 10 a Kwanan Bataru, wajen Fatika da ke karkashin karamar hukumar Giwa a jihar Kaduna.

Sannan har maboyar ‘yan bindigar ma ba ta tsira ba, sai da jami’an tsaron su ka banka ma ta wuta.

Kaduna: Jami'an tsaro sun kashe 'yan bindiga da dama, sun bankawa sansaninsu wuta
TaswirarJihar Kaduna. Hoto: The Punch
Source: UGC

Daily Trust ta ruwaito yadda ‘yan bindiga da dama su ka samu miyagun raunuka saboda musayar wutar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Read also

Bidiyon yadda jami’an yan sanda suka tsere yayin da yan bindiga suka mamaye fadar sarkin Ogun yayin taron APC

Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Kaduna, Samuel Aruwan ne ya bayyana hakan a wata takarda ta ranar Litinin.

A cewar sa, jami’an tsaron sun tseratar da wani Alhaji Abubakar Usman daga hannun ‘yan bindiga a yankin.

Ya ce ‘yan bindigan sun tsere sun bar baburan su

Aruwan ya kara da bayyana yadda wasu ‘yan bindiga su ka sha dakyar inda su ka tsere tare da manta babura, tociloli da layun su.

Akwai wani wuri da su ke zama, shi ma jami’an tsaro sun yi wa wurin kurmus da wuta.

A cewar sa bisa ruwayar Daily Trust, Gwamna Nasir El-Rufau ya yaba wa jami’an tsaron.

Sannan ya yi mu su fatan ci gaba da samun nasarar yakar ‘yan bindiga yadda ya dace.

Basarake a Arewa ya haramta bukukuwa cikin dare a ƙasarsa saboda harkokin ƙungiyoyin asiri

A wani rahoton, Mai garin Lokoja, Alhaji Mohammed Kabiru Maikarfi III, ya dakatar da yin duk wani sha’ani da dare a cikin garin Lokoja da duk wasu anguwanni da su ke da makwabtaka da Lokoja har sai yadda hali ya yi.

Read also

An kashe manoma uku a wani sabon hari da aka kai kan kauyen Filato

Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, ya bayar da umarnin nan ne sakamakon yadda ya ga bata gari su na amfani da damar shagulgulan dare wurin cutar da jama’a a cikin babban birnin jihar.

Kungiyoyin asiri su kan yi amfani da damar bukukuwan dare da sauran sha’anoni a Lokoja da kewaye wurin kai wa jama’a farmaki.

Source: Legit

Online view pixel