Bidiyon yadda jami’an yan sanda suka tsere yayin da yan bindiga suka mamaye fadar sarkin Ogun yayin taron APC

Bidiyon yadda jami’an yan sanda suka tsere yayin da yan bindiga suka mamaye fadar sarkin Ogun yayin taron APC

  • Wasu ‘yan daba sun kai mamaya wajen taron jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Ogun
  • Maharan sun far ma taron wanda ke gudana a wani dakin taro na fadar Oba Adedotun Aremu Gbadebo, Alake na Egbaland, a ranar Asabar, 16 ga watan Oktoba
  • An tattaro cewa jami'an tsaron da ke wajen sun tsere domin tsiratar da rayuwarsu a yayin tashin hankalin

Wani abun tashin hankali ya afku a fadar Oba Adedotun Aremu Gbadebo, Alake na Egbaland, a ranar Asabar, lokacin da ‘yan iska suka mamaye wajen taron jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na jihar da ke gudana.

Wani bangare na jam'iyyar APC a jihar ya yi hayar dakin taron a cikin fadar sarkin da ke Abeokuta, babban birnin jihar Ogun, a matsayin wurin gudanar da babban taronta.

Kara karanta wannan

Kano da sauran jihohi 7 da aka samu rabuwar kai a APC, aka zabi shugabanni 2 a jiha

Bidiyon jami’an ‘yan sanda da suka tsere yayin da ‘yan bindiga suka mamaye fadar sarkin Ogun yayin taron APC
Bidiyon jami’an ‘yan sanda da suka tsere yayin da ‘yan bindiga suka mamaye fadar sarkin Ogun yayin taron APC Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Daily Trust ta ruwaito cewa bangarori biyu na jam’iyyar a jihar sun yi shirin gudanar da taro iri daya.

Gwamna Dapo Abiodun da Sanata Ibinkunle Amosun, magabacinsa ne suke jagorantar bangarorin.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sai dai kuma, jim kadan kafin fara taron, ‘yan bindiga sun faso cikin dakin taron, wanda bangaren masu biyayya ga Amosun suke amfani da shi.

Jaridar ta kuma rahoto cewa daruruwan mutane da ke wajen, ciki harda jami’an tsaro sun tarwatse domin tsira a yayin da ake tsaka da hargitsin.

Magoya bayan jam’iyyar sun fatattaki ‘yan iskan da duwatsu

Daga bisani, taron magoya bayan jam’iyyar sun jefa duwatsu ga ‘yan daban wadanda daga bisani suka tsere suka bar wajen.

Sakamakon fusata da suka yi cewa jami’an tsaron da suka hada da ‘yan sanda da jami’an NSCDC basu iya jure ‘yan iskan ba, mambobin APC wadanda mafi akasarinsu matasa ne sun isa wajen jami’an tsaron sannan suka fatattake su.

Kara karanta wannan

Tsohon Kakakin majalisar dokoki da wasu jiga-jigai sun fice daga jam'iyyar APC, Zasu koma PDP

Amma kuma, jami’an tsaron, wadanda suka ci na kare, sun juya ga fusatattun matasa, inda suka yi harbi a iska domin hana ci gaban hare-hare.

Ga bidiyon a kasa:

Jam'iyyar APC ta dakatar da gangamin taronta a jihar Oyo

A wani labarin, Jam'iyyar APC mai mulkin ƙasar nan ta sanar da dakatar da gangamin taronta dake gudana yau a jihar Oyo saboda karya dokoki.

Rahoton dailytrust ya bayyana cewa APC ta ɗauki wannan matakin ne bisa samun bayanai cewa, "An ƙirƙiri wasu takardun da suka shafi taron na ƙarya da wasu dokokin da aka saɓa."

Gwamnan jihar Yobe kuma shugaban kwamitin rikon kwarya na jam'iyyar, Mai Mala Buni, shine ya bada wannan umarnin na gaggawa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel