An yanke wa Salisu ɗaurin gidan yari kan satar tukwane da kujeru a coci a Legas

An yanke wa Salisu ɗaurin gidan yari kan satar tukwane da kujeru a coci a Legas

  • Kotu a Legas ta yanke wa wani Ibrahim Salisu hukuncin daurin gidan yari saboda sata a coci
  • Yan sanda mai shigar da kara ya ce wanda ake zargin ya saci tukwane, kwanuka, kujeru da wasu kaya
  • Wanda ake zargin ya amsa laifinsa bayan an karonto masa hakan yasa aka yanke masa hukuncin dauri ba tare da zabin tara ba

Legas - Alkali a kotun majistare da ke zamanta a Surelere, Legas a ranar Juma'a ya yanke wa wani Ibrahim Salisu hukuncin daurin watanni shida saboda satar kayayyakin da kudinsu ya kai N300,000 daga cocin Deeper Life da ke kallon Aina Street, Surulere.

A cewar dan sanda mai shigar da kara, Sufeta Courage Ekhueorohan, wanda ake zargin, Salisu ya aikata laifin ne a ranar 2 ga watan Yuni, ruwaiyar NewsWireNGR.

Kara karanta wannan

Magidanci ya kashe matarsa saboda ta raina bajintarsa wurin kwanciyar aure

An yanke wa Salisu ɗaurin gidan yari kan satar tukwane da kujeru a coci a Legas
An yanke wa wani hukuncin dauri a gidan yari kan satan tukwane da wasu kaya a coci. Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Ya ce Salisu ya kutsa cikin cocin ya sace manyan tukwane biyu na aluminium, tukwanen soye-soye, kujerun roba biyar, kwanuka biyu da wasu karafa na mimbari da kudinsu ya kai N300,000.

Kamar yadda ruwayar ta NewsWireNGR ta bayyana, Alkalin kotun, Mrs M.I. Dan-Oni ya yanke wa wanda aka gurfanar hukunci bayan ya amsa aikata laifukan da ake tuhumarsa.

Dan-Oni wacce bata bashi zabin biyan tara ba, ta kuma kara masa da ayyuka masu wahala.

Wanda ake yanke wa hukuncin yana zaune ne a gida mai lamba 9, Seriki St., Idi-Araba, Mushin, Lagos kuma an gurfanar da shi a kotun ne a ranar 9 ga watan Yuli kan zargin sata.

Laifin sata ya saba wa sashi na 287 na dokar masu laifi na jihar Legas ta shekarar 2015.

Kara karanta wannan

Gas din girki ya fi karfin talakawa: 'Yan Benue sun rungumi aiki da icce da gawayi

Jerin sunayen 'yan Nigeria 11 da aka kama a Amurka kan almundahar kudi da damfarar mutane fiye da 50

A baya, kun ji cewa Hukumar binciken shari'a na Amurka ya gurfanar da wasu 'yan Nigeria 11 a kotu kan zarginsu da hada baki wurin aikata almundahar kudade, damfara ta banki da satar kudade da sunan wasu.

A ranar Laraba ne Attoni na Kudancin New York, Damian Williams da Jam'in FBI mai kula da New York, Patrick J, Freancy suka sanar da sunayen 'yan Nigeria 11 da ke da hannu wurin karkatar da miliyoyin daloli daga damfarar imel da damfarar soyayya.

Hukumar binciken shari'a na Amurka ta bayyana hakan a ranar Laraba kamar yadda ya zo a ruwayar SaharaReporters.

Asali: Legit.ng

Online view pixel