Majalisar tarayya ta sanar da ranar amincewa da kasafin kudi na 2022

Majalisar tarayya ta sanar da ranar amincewa da kasafin kudi na 2022

  • Majalisar tarayyan Najeriya ta ce ta aminta da kasafin kudin shekara mai zuwa tsakanin 12 zuwa 16 ga watan Disamba
  • Shugaban kwamitin kasafin, Sanata Barau Jibrin ne ya sanar da hakan ga manema labarai bayan zantawa da shugabannin kwamitocin majalisar
  • Dukkan ma'aikatu, bangarori da cibiyoyin gwamnati za su je su kare kasafin kudinsu a gaban majalisar tarayyan

FCT, Abuja - A ranar Litinin, majalisar dattawa ta ce za ta duba tare da amincewa da kasafin kudin shekarar 2022 tsakanin 12 ga watan Disamba zuwa 16 na 2021, Daily Trust ta wallafa.

Shugaban kwamitin majalisar dattawan kan kasafin, Sanata Barau Jibrin, ya bayyana hakan yayin zantawa da manema labarai jim kadan bayan ya gana da shugabannin sauran kwamitin majalisar.

Majalisar tarayya ta sanar da ranar amincewa da kasafin kudi na 2022
Majalisar tarayya ta sanar da ranar amincewa da kasafin kudi na 2022. Hoto daga dailytrust.com
Source: UGC

Dan majalisan ya ce sauraron kasafin daga ma'aikatu, bangarori da kuma cibiyoyi za a yi shi tsakanin ranar 18 ga watan Oktoba zuwa 5 ga watan Nuwamban shekarar nan.

Read also

Da duminsa: FG ta mika sabbin korafi 7 kan Nnamdi Kanu a gaban kotu

Ya ce kwamitocin majalisar za su mika rahotanninsu ga kwamitin kasafin a ranar 24 ga watan Nuwamba, Daily Trust ta wallafa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Tattaro rahotanni tare da shirya su wanda kwamitin kasafin zai yi za a fara shi daga ranar Alhamis 25 ga watan Nuwamba har zuwa Talata, 7 ga watan Disamba.
“Bugawa da rarrabawa zai biyo baya tsakanin ranar Laraba 8 ga watan Disamba zuwa ranar 13 ga watan Disamban 2021.
“Za a dawo da shi tare da gabatar da shi a ranar Talata, 14 ga watan Disamba yayin da za a duba tare da amincewa da shi tsakanin ranar Laraba 15 ga watan Disamba zuwa Alhamis, 16 ga watan Disamba," yace.

Dukkannin kasafin kudin shekarar 2022 kiyasin sa ya kai N16.39 tiriliyan.

Femi Adesina: FG na samun cigaba a fannin yakar rashin tsaro, jama'a ne ba su gani

Read also

Jerin matasan Najeriya 6 da suka hau kujerun gwamnoni, sun dauki tsauraran matakai

A wani labari na daban, mai magana da yawun shugaban kasa, Femi Adesina, ya ce gwamnatin tarayya ta na cigaba da samun nasarori kan yaki da rashin tsaro a kasar nan.

Har a yanzu, ana cigaba da samun matsalolin garkuwa da mutane, 'yan fashin daji da kuma harin da 'yan bindiga ke kaiwa a fadin kasar nan, TheCable ta ruwaito.

A yayin jawabi a ranar Litinin yayin tattaunawa da gidan Talabijin na Channels, Adesina ya ce duk wanda ke duba kokarin gwamnatin nan ba zai hada shi da na gwamnatin da ta gabata ba.

Source: Legit.ng

Online view pixel