Da duminsa: FG ta mika sabbin korafi 7 kan Nnamdi Kanu a gaban kotu

Da duminsa: FG ta mika sabbin korafi 7 kan Nnamdi Kanu a gaban kotu

  • Akwai yuwuwar shugaban 'yan awaren IPOB, Nnamdi Kanu, zai fuskanci sabbin tuhuma a ranar Alhamis, 21 ga watan Oktoba
  • Wannan rahotannin da ke zuwa suna bayyana cewa gwamnatin tarayya ta shigar da sabbin korafi 7 a kan Kanu
  • A daya bangare, Sanata Ifeanyi Ubah ya bukaci kotun da ke Abuja da ta bashi damar ganin Kanu wanda ke hannun DSS

FCT, Abuja - Gwamnatin tarayyar Najeriya ta mika gyararrun korafii 7 kan shugaban kungiyar 'yan awaren IPOB, Nnamdi Kanu, a gaban wata babbar kotun tarayya a Abuja.

Kamar yadda Daily Trust ta wallafa, sabbin korafe-korafen sun hada da ta'addanci tare da cin amanar kasa biyo bayan sauran korafin da ke gaban kotu tun 2016.

Da duminsa: FG ta mika sabbin korafe-korafe kan Nnamdi Kanu a gaban kotu
Da duminsa: FG ta mika sabbin korafe-korafe kan Nnamdi Kanu a gaban kotu. Hoto daga dailytrust.com
Source: UGC

Jaridar ta kara da cewa kotun ta sanar da ranar da za ta saurari koken, shi ne ranar Alhamis, 21 ga watan Oktoba.

Read also

Amurka ta gano sirri: 'Yan bindiga na hada kai da Boko Haram don bata gwamnatin Buhari

Takardar shari'ar wacce ke bayyana shari'a tsakanin gwamnatin tarayya da Nnamdi Kanu, an mika ta ga lauyan Kanu mai suna Ifeanyi Ejiofor da kuma masu gurfanarwa Shuaibu Labaran.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kamar yadda takardar ta bayyana, kotun za ta samu shugabancin mai shari'a Binta Nyako ne har a kammala shari'ar.

The Punch ta ruwaito cewa, daya daga cikin lauyoyin Kanu, Maxwell Opara ya yi magana kan gyararrun zargin.

Opara ya yi maganar ne a farfajiyar babbar kotun tarayya da ke Abuja yayin da ya raka Sanata Ifeanyi Ubah domin shigar da bukatar ganin Kanu a wurin jami'an tsaron farin kaya, DSS.

Sai dai kuma, har yanzu babu bayani dalla-dalla kan gyararrun korafin da aka mika gaban babbar kotun.

Hankula sun tashi, gagararren shugaban 'yan bindiga, Sububu ya koma Sokoto

A wani labari na daban, bayan watanni kadan da Bello Turji, shugaban 'yan bindiga ya bar sansaninsa da ke Zamfara zuwa Tozai a jihar Sokoto, wani gagararren dan bindiga, Halilu Bello Sububu ya tattara komatsansa tare da komawa dajin Sokoto.

Read also

Jerin sunaye: Manyan 'yan ta'adda da shugabannin 'yan bindiga 12 da aka sheke a 2021

Majiyoyi masu tarin yawa da suka hada da jami'an tsaron sirri, sun bayyana tunaninsu kan dalilin da yasa Sububu ya koma dajin Sokoto duk da sun ce wurin ya mayar sabuwar hedkwatarsa.

Dan ta'addan da ake zargin shi da shirya satar daliban kwalejin koyar da aikin noma da ke Bakura a jihar Zamfara, ya saci sama da mutum tamanin a kauyen Gora da ke karamar hukumar Maradun a jihar Zamfara.

Source: Legit.ng

Online view pixel