Femi Adesina: FG na samun cigaba a fannin yakar rashin tsaro, jama'a ne ba su gani

Femi Adesina: FG na samun cigaba a fannin yakar rashin tsaro, jama'a ne ba su gani

  • Femi Adesina, hadimin shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya ce gwamnatin tarayya na ganin cigaba a fannin tsaro
  • Kamar yadda Adesina ya bayyana yayin da ake tattaunawa da shi, ya ce duk wanda ke da ido zai ga kokarin da gwamnatin nan ke yi
  • A cewar Adesina, sun zo sun tarar da ta'addanci amma sun yi kokari wurin dakilewa wanda a yanzu haka ya yi sauki

Mai magana da yawun shugaban kasa, Femi Adesina, ya ce gwamnatin tarayya ta na cigaba da samun nasarori kan yaki da rashin tsaro a kasar nan.

Har a yanzu, ana cigaba da samun matsalolin garkuwa da mutane, 'yan fashin daji da kuma harin da 'yan bindiga ke kaiwa a fadin kasar nan, TheCable ta ruwaito.

Femi Adesina: FG na samun cigaba a fannin yakar rashin tsaro, jama'a ne ba su gani
Femi Adesina: FG na samun cigaba a fannin yakar rashin tsaro, jama'a ne ba su gani. Hoto daga thecable.ng
Source: UGC

A yayin jawabi a ranar Litinin yayin tattaunawa da gidan Talabijin na Channels, Adesina ya ce duk wanda ke duba kokarin gwamnatin nan ba zai hada shi da na gwamnatin da ta gabata ba.

Read also

Lai Mohammed: Babu dama-dama tsakanin 'yan bindiga da 'yan awaren IPOB

"Gwamnati a koda yaushe cigaba ta ke. Wata gwamnati na iya yin aiki mai kyau a wani bangare kuma ta gaza a wani bangare, za ta iya tafiya kuma wata gwamnati ta cigaba," yace.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kamar yadda Adesina ya kara da cewa:

"Za ku iya kwatanta halin da tsaro ke ciki a da, da yanzu? Ba zai yuwu ba. Daga 2015, akwai ta'addanci amma kwatsam bama-baman suka daina tashi a dukkan biranen kasar nan.
“Tabbas duk wanda ya ce ba a samu cigaba a wasu fannin tsaro ba, yaudarar kansa ya ke. Akwai wuraren da muka kawo sosai dai-dai gwargwado, akwai inda muka inganta sosai. Amma duk wanda ya ce mun gaza, ya shirga karya".

Hadimin shugaban kasa ya sanar da cewa:

“Akwai alkawurra uku manyan da muka yi kuma mun kara fadada su inda suka koma fannoni 9 da muka bai wa fifiko. Na farko kuwa shi ne tsaron kasa. Mun samu rashin tsaro kuma mun bibiye shi tare da kawo sauyi.

Read also

Buhari: Mu na da sabbin makaman yakar kowanne irin rashin tsaro

“Babbar matsalar yanzu ita ce 'yan fashin daji, garkuwa da mutane, kungiyoyin asiri da kuma duk wasu matsaloli da suka kunno kai. Babbar matsala ce amma gwamnati na kan ta kuma ana samun cigaba."

Buhari ya fara bincikar kwazon ministocinsa yayin da ake rade-radin zai kori wasu

A wani labari na daban, shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Litinin ya bude taron kwanaki biyu na duba kwazo da ayyukan ministocinsa a Abuja yayin da ake ta rade-radin zai sallami wasu ministocin kan rashin kwazo.

Taron wanda ya samu halartar ministoci, manyan sakatarorin gwamnati da sauran manyan jami'an gwamnati, taro ne da aka shirya domin duba yanayin ayyukan manyan masu mukamai a gwamnati, The Nation ta wallafa.

A ranar 1 ga watan Satumban da ta gabata, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanar da sallamar ministocinsa biyu a taron majalisar zartarwa ta tarayya.

Source: Legit.ng

Online view pixel