Amurka ta gano sirri: 'Yan bindiga na hada kai da Boko Haram don bata gwamnatin Buhari

Amurka ta gano sirri: 'Yan bindiga na hada kai da Boko Haram don bata gwamnatin Buhari

  • Wani kwamiti a kasar Amurka ya bankado cewa, akwai yiyuwar 'yan bindiga na hada kai da Boko Haram don bata gwamnatin Buhari
  • Wannan na zuwa ne cikin wani rahoton da wata jaridar Amurka ta fitar a ranar Asabar 16 ga watan Oktoba
  • A bangare, guda, gwamnatin Najeriya ta karyata wasu bayanai daga cikin rahoton jaridar ta kasar Amurka

Wani kwamitin kasar Amurka ya bankado yadda 'yan ta'addar Boko Haram da ke aiki a Arewa maso Gabas ke hada kai da 'yan bindiga da ke addabar al'ummomin Arewa maso Yamma don karbar kudin fansa daga gwamnatin Buhari da fararen hula

Wannan na zuwa ne daga cikin rahoton wata jaridar Amurka mai suna The Wall Street Journal a ranar Asabar 16 ga watan Oktoba.

Read also

NAF ta karyata rahoton biyan 'yan bindiga N20m don kada su harbo jirgin Buhari

Jaridar ta Amurka ta ba da rahoton cewa Amurka ba ta mai da hankali kan 'yan bindiga a matsayin barazana kai tsaye ga muradun ta ba, sai dai, jami'ai na sa ido kan kwamandojin 'yan ta'addan da ke hada kai da mayakan Boko Haram.

Amurka ta gano sirri, ta ce 'yan bindiga na hada kai da Boko Haram don bata gwamnatin Buhari
Wasu daga cikin 'yan ta'addan da suka addabi Najeriya | Hoto: independent.ng
Source: UGC

Rahoton na Amurka zai iya karfafa kiraye-kirayen da ake yi wa Shugaba Muhammadu Buhari na ayyana 'yan bindigan a matsayin 'yan ta'adda, duk da cewa ba su da wata manufar siyasa ko ta'allaka kansu da addini da suka bayyana.

Jami'an gwamnatin Najeriya sun ce gwamnati ba ta cikin gaggautar ayyana 'yan bindigan a matsayin 'yan ta'adda, amma ta umarci jami'an tsaro da su kara kaimin fatattakarsu a dazuzzuka da sauran maboyarsu.

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa, a wata hira da shugaba Buhari a farkon shekarar nan, ya bayyana cewa:

Read also

Zamfara: A kalla rayuka 12 sun salwanta, 'yan bindiga sun kone motar 'yan sanda

”Matsalar ita ce fahimtar al’adun makiyaya shanu, makiyaya shanu na Najeriya ba sa daukar komai sai sanda.
"Wani lokacin suna daukar adduna don yanko wasu ganyayyaki ga shanu, amma wadancan baki daga wasu sassan Afirka suna daukar AK-47.”

Sai dai, 'yan bindigar sun mallaki makamai fiye da AK-47, kuma kwanan nan sun harbo wani jirgin saman yaki da aka tura don gudanar da ayyukan leken asiri a yankin da ake rikici.

Jaridar ta kuma bayyana sakamakon binciken na Amurka cewa, rundunar sojin saman Najeriya ta biya kudi N20m don karbar bindigar harbo jirage daga hannun ‘yan bindiga kafin su yi amfani da ita wajen harbo jirgin shugaban kasa.

Sai dai, a wata sanarwa da hukumar sojin saman Najeriya ta fitar, ta karyata batun biyan kudin, inda ta bayyana cewa, bata cikin wata yarjejeniya da tsagerun, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Duk da cewa rundunonin sojin Najeriya na ci gaba da kai hari kan 'yan bindigan, har yanzu akan samu hare-hare a yankunan Arewa maso yamma daga 'yan bindigan.

Read also

Jerin matasan Najeriya 6 da suka hau kujerun gwamnoni, sun dauki tsauraran matakai

Sojoji na gina rugar Fulani a kudu: Rundunar soji ta yi martani kan jita-jita

A wani labarin, rundunar sojin Najeriya ta karyata jita-jitar da ke yawo mai cewa, a halin yanzu wata runduna na gina matsugunar Fulani a yankin kudu maso gabashin Najeriya.

Jita-jitar da ake yadawa ta ce, runduna ta 82 ta sojin Najeriya tana aikin gina rugar Fulani a tsakanin Ochima da Affa a cikin Igbo-Etiti da Udi na jihar Enugu.

A cikin wata sanarwar da Legit.ng Hausa ta samu a ranar Laraba 13 ga watan Oktoba dauke da sa hannun Manjo Abubakar Abdullahi, Mukaddashin Mataimakin Daraktan Hulda da Jama'a na Rundunar, rundunar sojin Najeriya ta watsi da batun.

Source: Legit

Online view pixel