Sojoji na gina rugar Fulani a kudu: Rundunar soji ta yi martani kan jita-jita

Sojoji na gina rugar Fulani a kudu: Rundunar soji ta yi martani kan jita-jita

  • Rundunar sojin Najeriya ta karyata jita-jitar da ake yadawa kan cewa, jami'an na gina rugar Fulani a kudu
  • A sanarwar da rundunar soji ta fitar, ta bayyana gaskiyar abin da sojojin ke ginawa a yankin kudu maso gabas
  • Rundunar ta yi kira da a gujewa dukkan labaran karya da ake yadawa tare da ta'allaka su ga rundunar

Rundunar sojin Najeriya ta karyata jita-jitar da ke yawo mai cewa, a halin yanzu wata runduna na gina matsugunar Fulani a yankin kudu maso gabashin Najeriya.

Jita-jitar da ake yadawa ta ce, runduna ta 82 ta sojin Najeriya tana aikin gina rugar Fulani a tsakanin Ochima da Affa a cikin Igbo-Etiti da Udi na jihar Enugu.

Sojoji na gina rugar Fulani a kudu: Rundunar soji ta yi martani kan jita-jita
Sojojin Najeriya | Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

A cikin wata sanarwar da Legit.ng Hausa ta samu a ranar Laraba 13 ga watan Oktoba dauke da sa hannun Manjo Abubakar Abdullahi, Mukaddashin Mataimakin Daraktan Hulda da Jama'a na Rundunar, rundunar sojin Najeriya ta watsi da batun.

Kara karanta wannan

NAF ta karyata rahoton biyan 'yan bindiga N20m don kada su harbo jirgin Buhari

A cewar sanarwar:

"Rundunar Sojin Najeriya ta 82 ta nuna damuwa matuka, kan zargi mara tushe da aka watsa ta wani haramtaccen gidan rediyo na yanar gizo cewa a halin yanzu Sashin Sojojin Najeriya na gina Ruga tsakanin Ochima da Affa a Kananan Hukumomin Igbo-Etiti da Udi, Jihar Enugu."

Sansanin horar da sojoji ake ginawa

Da take bayyana gaskiyar aikin da rundunar sojin ke yi a yankin, rundunar ta ce, injiniyoyinta na aiki ne a halin yanzu don gina wani sansanin horarwa na soji da za su zauna a yankin.

A cewar sanarwar:

"Injiniyoyin a halin yanzu suna gina cibiyar horar da sojoji a yankin Igbo-Etiti na karamar hukumar Udi, jihar Enugu.
"Bayan kammalawa, cibiyar za ta dauki sojoji a lokacin horo da taimako don inganta hanyoyin kare 'yan kasa masu bin doka a fadin Kudu maso Gabas."

Kara karanta wannan

Sojojin Najeriya sun fafata da Boko Haram, an ragargaji 'yan Boko Haram da yawa

Rundunar ta yi kira ga al'umma su guji wasu labaran karya da wasu makiya zaman lafiya a kasar ke yadawa.

Yadda 'yan sanda suka bindige mai sana'ar walda suka ce jagoran IPOB ne

A wani rahoton, Daily Trust ta ruwaito cewa, wani mazaunin jihar Imo, wanda ya shaida mutuwar Chigozie Nwaiwu, dan shekara 23 mai sana'ar walda, ya yi zargin cewa ‘yan sanda sun kashe shi tare da yi masa lakabi da jagoran IPOB.

A cikin wata sanarwa da ta fitar a makon da ya gabata, rundunar ‘yan sandan ta ce Uchenna Chukwu na Umunakanu a karamar hukumar Ehime Mbano ta jihar Imo da wani abokinsa sun yi artabu da su.

A cewar jami'in hulda da jama'a na 'yan sandan, CSP Mike Abattam, wanda ya fitar da sanarwar, mutanen biyu sun shiga hannun jami'an da suka kai hari a maboyarsu, a cikin artabun bindiga.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.