Yanzu-yanzu: Yan bindiga sun kai hari ofishin yan sanda, sun saki wadanda aka tsare sun kona motocin sintiri

Yanzu-yanzu: Yan bindiga sun kai hari ofishin yan sanda, sun saki wadanda aka tsare sun kona motocin sintiri

  • Wasu mahara da a yanzu ba a san ko su wanene ba sun kai hari caji ofis a jihar Ebonyi
  • Maharan da suka afkawa yan sandan cikin dare sun saki wadanda ake tsare da su a ofishin
  • Har wa yau, bata garin sun kuma kona motoccin sintirin yan sanda sannan sun raunata wasu jami'ai

Ebonyi - Wasu 'yan bindiga da ba a san ko su wanene ba, a ranar Litinin, sun kai hari hedkwatar yan sanda da ke karamar hukumar Ohaukwu da ke jihar Ebonyi.

A ruwayar SaharaReporters, 'yan bindigan sun kai harin ne misalin karfe 2 na dare inda suka saki dukkan wadanda ake tsare da su a ofishin yan sandan.

Kara karanta wannan

An kashe manoma uku a wani sabon hari da aka kai kan kauyen Filato

Yanzu-yanzu: Yan bindiga sun kai hari ofishin yan sanda, sun saki wadanda aka tsare sun kona motocin sintiri
Yan bindiga sun kai hari ofishin yan sanda, sun saki wadanda aka tsare sun kona motocin sintiri. Hoto: Daily Trust
Asali: Twitter

Maharan sun kuma kona wasu motoccin sintirin yan sanda sannan wasu jami'an yan sandan sun tsere da raunin bindiga.

A halin yanzu ba a kammala samun cikakken bayani kan wadanda suka kai harin ba.

Amma, kakakin yan sandan jihar Ebonyi, Loveth Odah ta tabbatarwa SaharaReporters afkuwar lamarin tana mai cewa kwamishinan yan sandan jihar ta tafi wurin don gane wa idonta.

Lamarin shine na baya-baya cikin jerin hare-haren 'yan bindiga da ke neman zama ruwan dare a yankin kudu maso gabashin Nigeria.

A baya-bayan nan gwamnonin yankin sun sanar da cewa za su kafa wata hukumar tsaro na hadin gwiwa mai suna 'Ebube Agu' don yaki da rashin tsaro da ke karuwa a yankin.

'Yan bindiga sun afka caji ofis, sun sace ƴar sanda da bindigu masu ɗimbin yawa

Kara karanta wannan

Zamfara: A kalla rayuka 12 sun salwanta, 'yan bindiga sun kone motar 'yan sanda

A wani labarin mai kama da wannan, an nemi wata jami'ar 'yan sanda an rasa bayan wasu 'yan bindiga sun kai hari caji ofis da ke Umulokpa a jihar Enugu a karamar hukumar Uzo-Uwani a jihar Enugu.

A ruwayar Daily Trust, Rundunar 'yan sandan ta tabbatar a ranar Litinin cewa wata 'yar sanda da ba a bayyana suna ta ba ta bata bayan harin da aka kai a ranar Asabar 9 ga watan Oktoban 2021.

An sace dukkan makaman da ke dajin ajiye makamai a ofishin 'yan sandan an kuma lalata na'urar CCTV da motoccin zuwa aiki na 'yan sandan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel