Babbar Magana: Hukumar Kwastam ta fallasa yadda yan sumogan shinkafa ke tallafawa yan bindiga a Katsina

Babbar Magana: Hukumar Kwastam ta fallasa yadda yan sumogan shinkafa ke tallafawa yan bindiga a Katsina

  • Hukumar kwastam (NCS) ta bankaɗo sirrin yadda yan sumoga ke kaiwa yan bindiga man fetur a jihar Katsina
  • Shugaban hukumar, Wada Chedi, yace da farko sun fara samun bayanan sirri amma daga bisani suka bi diddigin lamarin har suka tabbatar
  • A cewarsa yan sumoga na ƙara wa tankin mai girma sannan su cikashi a gidan mai sukai wa yan bindiga

Katsina - Hukumar kwastam ta ƙasa (NCS) reshen jihar Katsina ta bayyana cewa yan fasa ƙwaurin shinkafa na yin zagon ƙasa a yaƙin da ake da yan bindiga a Katsina.

Wada Chedi, muƙaddashin kwanturolan kwastan na jihar, shine ya bayyana haka a wata fira da manema labarai a ofishinsa ranar Litinin da yamma.

Premium times ta ruwaito shi yana cewa yan sumoga na taimakawa yan ta'addan wajen tsallake matakan da gwamnatin jihar ta ɗauka.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Dumi: 'Yan Bindiga Sun Kutsa Har Cikin Gida Sun Kashe Basarake da Wasu 2 a Jihar Arewa

Jihar Katsina
Babbar Magana: Hukumar Kwastam ta fallasa yadda yan sumogan shinkafa ke tallafawa yan bindiga a Katsina Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Yan sumoga na kaiwa yan bindiga fetur

Mista Chedi ya bayyana cewa masu aikin sumoga sun nemo sabbin hanyoyin kaiwa yan bindiga kayayyakin abinci da sauransu.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Yace yan fasa gwaurin na amfani da manyan tankuna domin ɗaukar man fetur su kaiwa yan ta'addan a cikin jeji, kamar yadda this day ta ruwaito.

Yace:

"Kwanan nan, mun kama motocin Peugeot 504, waɗanda yan sumogan suka kirkiri sabbin tankunan man fetur kuma suka cikasu taf da mai."
"Yan fasa kwaurin suna zuwa gidajen man fetur suna cika waɗannan tankunan, sannan su siyarwa yan bindiga."

Taya kwastam suka samu nasarar gano haka?

A cewar Chedi, hukumar kwastam ta fara samun bayanan sirri kan irin wannan ayyukan da yan fasa kwaurin suka fara.

"Mun fara samun bayanan sirri, daga nan muka sa musu ido tun daga inda suke siyan man fetur ɗin har zuwa inda suke siyarwa yan bindiga."

Kara karanta wannan

Bayani Kan Yadda Na Cika Alkawuran Da Na Yiwa Yan Najeriya Cikin Shekaru 7, Buhari

"Amma suna fahimtar ashe mun biyo su, domin suna da wayo, nan take suka bar motocin suka tsere, muka kwace motocin."

A wani labarin kuma Miyagun yan bindiga sun bude wa masallata wuta, Sun kashe aƙalla 10 a jihar Katsina

Dailytrust ta rahoto cewa lamarin ya auku ne lokacin da mutanen ke tsaka da sallar Magrib ba zato yan bindigan suka buɗe musu wuta, ranar Talata.

Legit.ng Hausa ta gano cewa tuni aka gudanar da jana'izar waɗanda suka rasu da safiyar ranar Laraba, yayin da waɗanda suka ji raunuka aka kaisu asibiti.

Asali: Legit.ng

Online view pixel