Pandora: EFCC ta yi wa Peter Obi kiran gaggawa kan kamfanoninsa na ketare

Pandora: EFCC ta yi wa Peter Obi kiran gaggawa kan kamfanoninsa na ketare

  • Hukumar yaki da rashawa da hana yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, ta bukaci ganin Peter Obi a ofishin ta
  • Hakan an gano ya na da alaka ne da binciken Pandora da ya fallasa yadda dan siyasan ya kwashi kudin kasa ya auna Turai
  • An gano cewa, fadar shugaban kasa ta bukaci a binciki dukkan 'yan siyasan da harkallarsu ta bayyana a binciken Pandora

Tsohon gwamnan jihar Anambra, Peter Obi, wanda a sirrance ya mallaki kamfanoni a ketare ya na daga cikin 'yan siyasar Najeriya da Premium Times ta ruwaito.

Hukumar yaki da rashawa tare da hana yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, ta kira tsohon gwamnan domin ya amsa tambayoyi.

Pandora: EFCC ta yi wa Peter Obi kiran gaggawa kan kamfanoninsa na ketare
Pandora: EFCC ta yi wa Peter Obi kiran gaggawa kan kamfanoninsa na ketare. Hoto daga premiumtimesng.com
Asali: UGC

Wannan ne karon farko da hukuma a Najeriya za ta fara bincikar daga cikin wadanda aka fallasa harkallar wawura da adana kudade a kasashen ketare da suka yi ta binciken Pandora.

Kara karanta wannan

Ba guduwa zan yi ba: Sheikh Zakzaky ya zargi gwamnatin Buhari da hana shi sakat

Wata majiya ta tabbatar da cewa fadar shugaban kasa ta bayar da umarnin cewa a binciki duk wadanda sunansu ya fito a wannan binciken.

Premium Times ta gano cewa, hukumar EFCC ta gayyaci Obi cikin makon nan kuma an bukaci ya kai kan shi hedkwatar hukumar da ke Abuja a ranar 27 ga watan Oktoba domin ya gana da masu bincike.

Majoyoyi sun ce wannan gayyatar ta na da alaka da fallasar da Pandora Papers ta yi. Rahoto ya fallasa yadda Obi ya adana wasu dukiyoyi a kasashen ketare wandanda ya ki bayyanawa yayin da ya ke gwamna.

Duk wadanda harkallar kudaden da aka bankado, sun yi karantsaye ga dokokin kasar nan wadanda aka gindayawa jami'an gwamnati, duk da Obi ya cigaba da ikirarin cewa bai yi wani abun ashsha ba.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya magantu kan titsiye shi da hukumar EFCC ta yi

EFCC ta gurfanar da Yarima a gaban kotu kan badakalar N35.5m

A wani labari na daban, hukumar yaki da rashawa da hana yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, reshen Ibadan a ranar Talata, ta gurfanar da yariman Owo, Touluwalade Olagbegi.

An gurfanar da yariman a gaban mai shari'a Uche Agomoh a babbar kotun tarayya da ke zama a Ibadan kan laifin samun kudi har miliyan talatin da biyar ta hanyar karya.

Ana zargin yariman Owo na jihar Ondo, wanda ke zama a Bodijia, da karbar kudi har N35 miliyan daga mai korafin kan cewa za su yi kasuwancin forex, EFCC ta wallafa a shafin ta na Facebook.

Asali: Legit.ng

Online view pixel