Kwankwaso ya magantu kan titsiye shi da hukumar EFCC ta yi

Kwankwaso ya magantu kan titsiye shi da hukumar EFCC ta yi

  • Sanata Kwankwaso ya karyata rade-radin da ke yawo na cewa hukumar EFCC ta yi ram da shi
  • Tsohon gwamnan Kanon ya ce da kan shi ya je hukumar domin wanke kansa a wani korafi
  • A cewar shugaban Kwankwasiyyar, 'yan siyasa masu son ganin sun tozarta shi ne suka kai karar

Tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, ya musanta labaran da ke yawo a kafafen yada labarai kan cewa hukumar yaki da rashawa, EFCC, ta yi ram da shi.

Tsohon gwamnan ya tabbatar da cewa, da kan shi ya kai wa hukumar ziyara har ofishinsu domin wanke sunansa kan wani korafi da aka kai gaban ta a kan shi, Daily Nigerian ta ruwaito.

Kwankwaso ya ce ya ziyarci hedkwatar hukumar domin ya sanar da abinda ya sani kan zargin, inda ya kara da cewa da kan shi ya je hukumar kuma ya gana da wasu jami'an hukumar na wasu sa'o'i.

Kara karanta wannan

Pandora: EFCC ta yi wa Peter Obi kiran gaggawa kan kamfanoninsa na ketare

Kwankwaso ya magantu kan titsiye shi da hukumar EFCC ta yi
Kwankwaso ya magantu kan titsiye shi da hukumar EFCC ta yi. Hoto daga dailynigerian.com
Asali: UGC

Kwankwaso, tsohon ministan tsaro, ya kwatanta korafin da zugar 'yan siyasa tare da zargin cewa 'yan siyasan da ke son ganin sun tozarta shi ne suka kai korafin.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kamar yadda Daily Nigerian ta wallafa, ya ce ko kadan babu kamshin gaskiya a zargin.

"Rade-radin kama ni da aka yi ba shi da tushe balle gaskiya. A matsayi na na dan kasa nagari mai kiyaye doka, da kai na na ziyarci hukumar a ranar Lahadi domin wanke kai na kuma babu shakka hakan ne ya faru".
"Na hadu da jami'an EFCC kuma na ce zan wanke sunana ne kan korafin da aka rubuta a kai na tun shekara shida da ta gabata. Na samar da ansoshi kan duk tambayoyin da aka yi min," tsohon gwamnan yace.

Hon Sha'aban: Da a yau za a yi zaben gwamna a Kano, warwas za a yi wa APC

Kara karanta wannan

An kashe manoma uku a wani sabon hari da aka kai kan kauyen Filato

A wani labari na daban, Honarabul Sha'aban Sharada, dan majalisar wakilai kuma mamban jam'iyyar All Progressives Congress (APC) daga Kano, ya ce jam'iyyarsu ba za ta iya cin zaben gwamnoni ba a Kano a halin da ake cikin.

Dan majalisan ya sanar da hakan ne a wata tattaunawa da aka yi da shi da BBC kan rikicin da ya sarke jam'iyyar a Kano.

Ya ce rikicin da ake ciki ne yasa suka yi wani taron masu ruwa da tsaki a gidan Sanata Ibrahim Shekarau a ranar Talata. Bayan taron, 'yan majalisar sun rubuta korafi tare da mika shi ga shugaban jam'iyyar na rikon kwarya, Gwamna Mai Mala Buni.

Asali: Legit.ng

Online view pixel