EFCC ta gurfanar da Yarima a gaban kotu kan badakalar N35.5m
- A ranar Talata da ta gabata, EFCC ta gurfanar da Yarima Toluwalade Olagbegi a gaban wata kotu a Ibadan
- Kamar yadda aka karanto, ana zargin yariman da damfarar wani dan kasuwa N35.5 miliyan a kasuwancin forex
- Duk da musanta zargin da ake masa, Mai shari'a Agomoh ya bukaci a adana yariman a gidan gyaran hali har zuwa 25 ga watan nan
Ibadan - Hukumar yaki da rashawa da hana yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, reshen Ibadan a ranar Talata, ta gurfanar da yariman Owo, Touluwalade Olagbegi.
An gurfanar da yariman a gaban mai shari'a Uche Agomoh a babbar kotun tarayya da ke zama a Ibadan kan laifin samun kudi har miliyan talatin da biyar ta hanyar karya.
Ana zargin yariman Owo na jihar Ondo, wanda ke zama a Bodijia, da karbar kudi har N35 miliyan daga mai korafin kan cewa za su yi kasuwancin forex, EFCC ta wallafa a shafin ta na Facebook.
Tuhumar an karanto ta kamar haka:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Cewa kai, Toluwalade John Olateru-Olagbegi a ranar 4 ga watan Maris na 2021, a cikin garin Ibadan, ka karba N35 miliyan daga wani dan kasuwan Najeriya mai suna Julius Olorunsogo Alase.
"Ka karba kudin a madadin Lusan Royal Trading cike da karya kan cewa ya na daga cikin kudin da zai biya kafin a turo masa wasu dala miliyan daya daga Amurka.
"Hakan ya ci karo da sashi na 1, sakin layi na daya kuma abun hukuntawa karkashin sashi na 1, sakin layi na uku na dokokin manyan laifuka da al'amura masu alaka da damfara na 2006”.
Mai kare kansa ya musanta aikata laifin da ake tuhumarsa yayin da aka karanto masa zarginsa da ake.
Mai shari'a Agomoh daga nan ya bukaci a adana masa yariman a gidan gyaran hali da ke Agodi tare da dage shari'ar zuwa ranar 25 ga watan Oktoba domin sauraron bukatar beli da kuma ranar 15 ga watan Nuwamba domin cigaba da shari'ar.
EFCC ta gurfanar da tsohon shugaban jami’a kan badakalar N260m
A wani labari na daban, hukumar yaki da rashawa tare da hana yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa a ranar 12 ga watan Oktoban 2021 ta gurfanar da tsohon shugaban jami'ar gwamnatin tarayya da ke Gusau, Farfesa Magaji Garba.
EFCC ta gurfanar da tsohon malamin makarantar ne a gaban Mai shari'a Maryan Hassan Aliyu ta babbar kotun tarayya da ke Jabi a Abuja.
Kamar yadda hukumar ta bayyana, ana zarginsa ne da laifuka biyar da suka hada da samun kudi ta hanyar karya, damfara tare da takardun jabu.
Asali: Legit.ng